Connect with us

Nasarorin Ganduje

Gwamna Ganduje ya cikawa Kanawa alkawuran da yayi musu

Published

on

YADDA GWAMNA GANDUJE YA CIKA AL’ƘAWURA JIHAR KANO TA ZAMTO ABAR ALFAHARI A DUNIYA GABA ƊAYA

SHARHI: Daga Bashir Abdullahi El-bash

Yau Lahadi 27 ga watan Octoba, 2019.
Kamar yadda mu ke ƙoƙari da gwagwarmayar nazari da adana dukkan tsare-tsare da manufofi gami da ayyuka, mu na kallon mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mai himma da ƙoƙarin samar da sabbin tsare-tsare cikin hanzari fiye da duk yadda mu ke tsammani.

A kusan kowacce daƙiƙa ɗaya ta agogo, gwamna Ganduje ya kan yi tunani kan yadda zai kai Jihar Kano kan mataƙin ƙololuwar nasara ta fuskar tattalin arziƙi da kyautata walwala da kuma haɓaka cigaba mai ɗorewa a kowane fanni na rayuwar ɗan adam.

Ga waɗanda su ka san shi tuntuni, gwamna Ganduje alama ne da ke nuni da yadda ya ke da himma kan halartar dukkan wasu muhimman al’amura kan sha’anin gwamnati da cigaban al’umma.

Wani ƙarin muhimmin al’amari ga gwamna Ganduje shi ne yadda ya ke bin koyarwa addinin Musulunci wajen cika dukkan alƙawuran da ya ɗauka.

Hujja a kan hakan, yanzu zan gabatar muku wasu daga cikin alƙawuran da ya yi ya kuma cika su da kuma waɗanda su ke kusa da cikawa.

Gwamna Ganduje ya raba tufafin sanyawa na makaranta (Uniforms) ga ɗalibai kimanin (779,522).

A wani mataki na murnar da Duniya ta ke yi masa game da shirinsa na fara bayar da ilimi kyauta kuma wajibi, gwamna Ganduje ya raba kayan makaranta da kayayyakin koyo da koyarwa ga ɗalibai da makarantu firamare fiye da guda (1,180) a Jihar Kano.

Kamar yadda gwamna Ganduje ya bayyana, hakan zai taimaka wajen ƙarfafar gwiwar iyaye da majiɓinta lamuran yaran su riƙa sanya yara a makarantu ba tare da wata fargaba kan kuɗin makaranta ba.

Kamar yadda ya yi alƙawari tuni ayyuka sun kankama.

Gwamna Ganduje ya ƙaddamarwar da rabon kayan makarantar a ranar Alhamis, 24 ga watan Octoba, 2019, a makarantar Firamare ta Mariri, wato(Mariri Special Primary School) da ke ƙaramar hukumar Kumbotso.

Kamar yadda aka ƙaddamar da wannan, haka mai girma gwamna zai cigaba da zagayawa sannu a hankali har sai ya gama da dukkan ƙananan hukumomin Jihar Kano guda (44) gaba ɗaya.

Kimanin kayan sawa na makaranta (Uniforms) guda (29,480) mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya raba ga ɗalibai ƴan aji (1) na dukkan makarantun Firamare guda (78) da ke ƙaramar hukumar ta Kumbotso.

A fannin kayan aiki na koyo da koyarwa:

mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya raba Littattafai na aiki guda (500) da kuma Littattafan karatu na Hausa guda (500) da kuma (Flash Card) guda (50).

A ya yin da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron ƙaddamar da rabon kayan:

Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa: “tuni gwamnatin Jihar Kano ta fara tura kuɗaɗe cikin asusun ajiyar Banki na makarantun Firamare da na Sakandire guda (1,180) masu jimillar ɗalibai guda (834, 366) inda za su riƙa samun kimanin (Naira Miliyan 200) a duk ƙarshen wata, inda ya kama (Naira Miliyan 2.4) a duk shekara”.

Sannan kuma, gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta sake: Samar da sabbin kayan sawa na makaranta (Uniforms) ga sabbin ɗalibai maza da mata kimanin guda (779,522) a kan kuɗi kimanin (Naira Miliyan 381).

Samar da sabbin asibitoci da za su ci gadaje a ƙalla guda (400) a kowacce masarauta ɗaya cikin huɗun da ya samar:

Jim kaɗan bayan sanar da sabbin masarautun Rano da Bichi da Ƙaraye da Gaya, gwamna Ganduje ya yi alƙawarin samar da asibitoci domin rage cinkoso a asibitocin masarautar Kano da kuma kyautata harkokin lafiya ga al’umma a kusa da su.

Gwamna Ganduje ya bayyana wannan alƙawari ne a ranar 6 ga watan Yuli shekarar 2019, a ya yin wata ziyara da ya kai fadar mai martaba sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar (Autan Bawo),

“gwamnatina ta himmatu wajen kyautata fannin kiwon lafiya a kowacce masarauta. Kuma tuni kiwon lafiya a Jihar Kano ya hau matakin tserewa tsara wajen inganci, za mu cigaba da yin duk mai yiwuwa wajen ɗorewar wannan nasara da mu ka samu”.

Kuma a cikin ƙasa da ƴan watanni da yin wannan alƙawari, tuni gwamna Ganduje ya gayyaci ƴan kwangila domin fara aikin samar da asibitin a sabbin masarautun 4.

Kamar yadda gwamna Ganduje ya bayyana, Gwamnatinsa ta “gayyaci fitattun ƴan kwangila da su nuna sha’awarsu ta neman aikin samar da asibitoci guda (4) waɗanda za su ci gadaje guda (400) a dukkan manyan biranen sabbin masarautu huɗu (4) na Jihar Kano”

“Awai tsarin da ake da shi tun a baya, amma za mu samar da ingantaccen gyara akai”. Inji Gwamna Ganduje.

“Za mu tabbatar da an bi duk wata ƙa’ida domin tabbatar da adalci da gaskiya cikin aikin, kuma hakan wata alama ce da ke tabbatar da cika alƙawarin da mu ka yi na kyautata fannin lafiya a masarautun”.

“Jihar Kano za ta ƙara ƙaimi wajen ƙara haɓaka sha’anin kiwon lafiya a dukkan sabbin masarautunmu huɗu. Kowacce asibiti ɗaya za ta ɗauki gadaje a ƙalla guda (400) na kwantar da marasa lafiya”.

Za a samar da gadaje 22, da wurin ba da agajin gaggawa ga masu hatsari (A.E) da wurin yin tiyata, da ɗakin haihuwa da ɗakin lura da masu lalurar ido da kunne, da hanci da haƙori.

Sauran kayayyakin da za a samar sun haɗa da: gina wajen (Physiotherapy), da na (Radiology) da wurin gwaje-gwajen jini, ?Laboratory), da na ajiye gawa (Mortuary), da kuma wurin cin abinci (Restaurants/Eateries), sai kuma (Patient Relation Sheds).

Da kuma banɗakunan manyan (VIP), sai kuma (Road networks) tare da (external works), da kuma (Entrance Gates), haɗe kuma da samar da wutar lantarki da gadajen kwanciyar malaman jinya sai (Generating Sets), da kuma gidajen malaman jinya da sauran ma’aikata.

A cibiyar kula da masu cutar kansa, gwamna Ganduje ya yi alƙawarin samar da ingantattun kayan aiki irin na zamani.

Kuma cibiyar za ta zama kwatankwacin irin ta sauran ƙasashen duniya wacce kuma babu kamarta a duk faɗin Nageriya.

Duba da yadda a kullum ake cigaba da samun yawaitar masu fama da wannan lalura tare da fatan ganin an rage matsalar domin ƙara kyautata sha’anin kiwon lafiya a Jihar, tare da bin dukkan matakan da su ka kamata.

Kayayyakin da ake buƙata sun haɗa da:

Na’urorin: (True Beam Linear Accelerator) guda 1, da (Halcyon Linear Accelerator) shi ma guda 1, sai (GammaMed plus Brachytherapy hardware and Applicator) guda 1.

Tare da (ARIA Radiation Oncology) guda 1, sai (TPS Eclipse Integrated with ARIA) guda 1 tare kum da (Complete Dosimetry Tools) guda 1.

Sauran sun haɗa da (GE 16 Slices CT Stimulator) guda 1, da (GE High Resolution Ultrasound) guda ɗaya, da kuma (GE C-Arm) sai kuma injin gano cuta ta ɓoye (Xray machine) guda ɗaya.

Sai kuma kayayyakin ba da agajin gaggawa, (Defibrillator) guda biyu, da injin shaƙar numfashi (Oxygen Concentrator) guda 2.

Sai kuma (Suction Machine) shi ma guda 2, (Laryngoscope) guda 2, da kuma injin bibiyar halin da marar lafiya ya ke ciki guda 1 tare kuma da Nebulizer guda biyu.

Sai kuma injinan wutar lantarki mai ƙarfin (750 KVA) guda 1, da mai ƙarfin (500KVA) shi ma guda 1, da kuma mai ƙarfin (160 KVA UPS) guda 1, da kuma faya-fayan samar da wuta mai amfani da hasken rana.

Da kuma kayan aiki a ɗakin gwaje-gwajen jini da kuma kayan ƙawa na cikin asibitin gaba ɗaya. Da kuma sauran kayayayyaki na ɗakin gwaje-gwajen jini da na cikin asibitin gaba ɗaya.

Wannan shi ne ke ƙara shaidawa duniya yadda Jihar Kano ta yi dace da shugaba mai cika alƙawari.

Yunƙurin samar da RUGAR zamani, “shugaban fulani makiya”.

Ba shakka gwamna Ganduje ya cancanci wannan laƙabi na “shugaban fulani makiyaya” da ƴan Nageriya su ka laƙaba masa. Duba da dukkan Nageriya da ma nahiyar Afrika gaba ɗaya babu wani shugaba da ya ke ƙoƙari da gwagwarmayar kare haƙƙin fulani makiyaya da ya wuci gwamna Ganduje.

Domin tun a lokacin da gwamnatin tarayya ta yi ƙurin samar da ruga gwamna Ganduje ne ya ce lallai sai an yi a duk Jihohi ko da kuwa Jihohin ba na Fulani ba ne, sannan shi zai yi a Jihar Kano ga duk fulani makiyaya babu waraki.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamiti a ranar 18 ga watan Ogusta, 2019, domin su gudanar da bincike kan wuri da kuma nazarin abubuwan da ake buƙata wajen samar da rugar zamani ga fulani makiyaya a Jihar Kano.

Kwamitin mai ɗauke da mutane (26), ƙarƙashin jagorancin Dakta Jibirilla Muhammad, ya ƙunshi masana da ƙwararru a fannoni daban-daban, kama daga kan jami’an tsaro, da likitocin dabbobi, da fulani makiyaya, da malaman makaranta da sauransu.

Kuma bayan shafe tsawon watanni (6) su na aikin binciken a ranar 14 ga watan Satumba, 2019, kwamitin ya miƙa rahoton bincikensa ga mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a zauren majalissar zartarwa na jiha da ke fadar gwamnatin Jihar Kano.

Da ya ke jawabi ya yin karɓar rahoton, mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa:

“Batun samar da tsaro da zaman lafiya, ya na ɗaya daga cikin manyan dalilai na farko wajen samar da rugar zamani ga fulani makiyaya”.

“Za mu canza tunaninsu daga rungumar kiwo a matsayin batun al’ada zuwa na tattalin arziƙi, domin amfanin kansu da Jihar Kano da kuma ƙasa gaba ɗaya”

“Ka da ku damu kan ku da batun ruga ko duk wani suna da su ke kiranta, a taikace dole fulani makiyaya su zauna wuri ɗaya su kuma amfani dukkan wasu kayayyakin more rayuwa kamar kowane ɗan ƙasa”.

“Su na buƙatar samun ilimi, domin ilimi makulli ne. Dan haka su na buƙatarsa, shikkenan. Mu na kuma tunanin samar da mayankar dabbobi ta zamani, ta yadda za mu na tura shanu daga Arewa zuwa Kudu a madadin yadda ake zirga-zirga da su”.

“Kuma a kan hakan mu na tattaunawa da Bankin samar da cigaba na Musulunci, tuni kuma tattaunawar tamu ta yi nisa, yanzu haka mu na kan matakin fara aiwatarwa cikin haɗin gwiwa”. Inji Gwamna Ganduje.

Shi ma a nasa jawabin a ya yin miƙa rahoton ga mai girma gwamna, shugaban kwamitin, Dakta Jibilla Muhammad, ya bayyana cewa:

“mai girma gwamna, Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancinka, ita ce Jiha ta farko wacce ta fara rungumar wannan aniya da ta haifar da ruɗani ta samar da rugar zamani ga fulani makiyaya a duk Nageriya”.

“mai girma gwamna, a ya yin da sauran takwarorinka su ka nuna ƙyama kan wannan aniya ta zamanantar da tsarin kiwon dabbobi, kai kuwa sai ka kalli ƙudurin a matsayin wani al’amari da zai taimaki cigaban tattalin arziƙi, sannan ka yi watsi da duk wata farfaganda da aka yi ta yaɗawa kan ƙyamatar wannan aiki, kafa wannan kwamiti da ka yi, shi ya ƙara bayyana himmatuwarka kan wannan aiki”.

“kafin mu cimma matsayar da mu ka ɗauka, mun ziyarci dazuka har guda (5) da ke sassa daban-daban na Jihar Kano. Dazukan, sun haɗa da:

“Dajin Dansoshiya, wanda ke ƙaramar hukumar Ƙiru, da dajin Fanyabo, wanda ke ƙaramar hukumar Doguwa, da dajin Duddurum Gaya, wanda ke ƙaramar hukumar Ajingi, da Dajin Dunawa, wanda ke ƙaramar hukumar Maƙoda, sai kuma wasu yankuna na ƙaramar hukumar Bichi”.

“Daga ƙarshe mun cimma matsaya kan zaɓar dajin Dansoshiya a matsayin inda za a tsugunnar da fulani makiyaya.

“Biyo bayan dogon nazari cikin nutsuwa da tattaunawa gami da bin diddigi da aunawa, gami da duba da manufofi da burukan da gwamnati ta ke da su kan wannan aiki, kwamitinmu ya zaɓi dajin Dansoshiya na ƙaramar hukumar ƙiru, a matsayin wurin da gwamnati za ta ƙaddamar da wannan aiki”.

“Dajin Dansoshiya, daji ne mai amfani da girma matuƙa, ta yadda zai iya ɗauke adadin fulani makiyayan da za a tsugunnar, da kuma wadatacciyar ƙasar kiwo”.

“Fuskokin dajin da kuma yadda ya ke da wadataccen yanayin samar da ruwa, a nan ne ya kyautu a samar da wannan ruga, mun ji a ranmu cewa mun yi kykyawan zaɓi”.

Kuma kamar yadda mai girma gwamna ya umarce su a lokacin da ya ƙaddamar da su a matsayin kwamitin, da su kawo masa zanen taswira na rugar da kuma kasuwar saida nono gaba ɗaya, tuni sun cika wannan umarni.

shugaban kwamitin, ya kuma bayyana cewa za su ɗauki masu ilimin gine-gine, domin su tsara musu gida na zamani mai ɗauke da ɗakuna biyu, wanda zai kasance kamar rukuni-rukuni tare da gidaje shida a kowane rukuni. A ya yin ziyarorin da su ka kai, shugaban kwamitin ya bayyana cewa duk inda su ka je su na tuntuɓar dukkan masu ruwa da tsaki ciki kuwa har da manoma da makiyaya.

“Sannan kwamitin ya yi duba kan buƙatar samar da madatsun ruwa da asibitin dabbobi, da wurin shan magani, da cibiyar tattara nono, da makarantun boko da na islamiyya da masallaci da ƙaramin ofishin ƴan sanda, kuma duk waɗannan su na cikin taswirar da su ka tsara”.

“la’akari da yanayin ƙasa da tsarin Dajin Dansoshiya, mun cimma matsaya kan ciyawar (Napia) a kan sauran ciyayin.

“A fannin samar da kasuwar nono kuwa, mun gama nazari mun cimma matsaya kan samar da kasuwar a yankin dajin Ɗangwauro. Nan ne wurin da ya kamata a samar da kasuwar nono, saboda muhimmancin samun tantancewa musamman daga yankin samar da nono na Tudunwada da Doguwa, da Gwarzo, kusa da yankin titin zuwa Maiduguri.

A tsarin samar da kasuwar nonon, kwamitin ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar samar da ɗakunan sanyaya nono, da ɗakunan ajiya, gami kuma da makewayi, (banɗakuna).

Kuma tuni gwamna Ganduje ya yi nisa kan nazarin rahoton wannan kwamitin bincike domin ganin Rugar ta kankama an tsugunnar da fulani makiyaya a wuri guda.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Nasarorin Ganduje

Za’a kaddamar da gidan rediyon gwamna Ganduje da zaku iya sauraro daga ko ina a duniya

Published

on

By

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Duk Nageriya, Gwamna Ganduje Ne Gwamna Ɗaya Tilo Da Aka Taɓa Samar Masa Gidan Rediyo A Yanar Gizo-Gizo.

-Gidan Rediyo Ne Da Zai Riƙa Gabatar Da Shirye-Shiryensa Kai Tsaye Har Tsawon Awanni Ashirin Da Huɗu Dare Da Rana A Kowacce Rana A Duk Mako.

-Sannan Kuma, Gidan Rediyon Zai Kasance A Ƙarƙashin Kulawar Ƙungiyar Ganduje New Media Promoters.

Yau Laraba, 20 ga watan Nobemba, 2019.
A wani mataki na cigaba da ƙara sanar da duniya ɗumbin ayyukan da mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya aiwatar a zangon farko na gwamnatinsa da kuma waɗanda ya ke cigaba da aiwatarwa a wannan zangon mulki na biyu, da kuma ƙoƙarinmu na ƙara himma wajen cigaba da ƙara ɗaga kima da darajarsa (gwamna Ganduje) a idon duniya, tuni mun kammala samar da katafariyar kafar watsa labarai ta Rediyo wacce za ta riƙa aiki na tsawon a wanni (24) a kowacce rana kai tsaye (Online).

Duk da kasancewar akwai ƴan gyare-gyare da mu ke cigaba da yi wa tashar a halin yanzu domin ƙara kyautata jin daɗin masu sauraro, cikin ikon Allah mu na farin cikin ƙaddamar da fara amfani da gidan Rediyon tayadda duk wanda ya buga adireshinmu na: www.gandujeonlinerediyo.com, zai zame mu kai tsaye.

Wannan ƙaddamarwa ce ta yadda mutane za su fara amfani da gidan Rediyon kai tsaye, daga bisani kuma akwai gagarumin taro na musamman da za mu shirya domin ƙaddamar da wannan gidan Rediyo a zahiri. Tayadda kuma hatta mutanen karkara da ke amfani da wayoyin hannu ƙanana ma za su iya kama gidan Rediyon su kuma saurari shirye-shiryenmu kai tsaye.

Haka zalika, gidan Rediyon zai kasance ne a ƙarƙashin kulawar ƙungiyar Ganduje New Media Promoters, a wani mataki na zaburar da matasa sanin amfani da fasahohin zamani da aikace-aikacen kimiyya da fasaha.

Mun tanadar muku shirye-shirye na musamman masu armashi da gamsarwa kan ɗumbin nasarori da managartan ayyukan mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sannan akwai ɗumbin waƙoƙi na mawaƙan mai girma gwamna daban-daban waɗanda su ma za mu riƙa sanya muku domin ƙayatar da ku da kuma ɗebe muku kewa a kowane lokaci.

Ganduje Online Rediyo ita ce kafar watsa labarai ta farko mai watsa shirye-shiryenta kai tsaye wacce aka taɓa samarwa wani gwamna a tarihin gwamnonin Nageriya gaba ɗaya na da da na yanzu. Za ku iya sauƙe manhajarmu a Play Store, ko ku latsa wannan kai tsaye domin sauƙewa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.gandujeonlineradio.com

Mu na fatan jama’a za su rungumi wannan gidan Rediyo hannu bibbiyu domin samun ƙayatattun shirye-shirye masu armashi da gamsarwa gami kuma da ƙayatarwa a kowane lokaci. Mun gode.

Continue Reading

Nasarorin Ganduje

An zabi gwamna Ganduje uban kungiyar Fulani ta Africa

Published

on

By

ƘUNGIYAR FULANI MAKIYAYA TA NAHIYAR AFRIKA TA ZAƁI GWAMNA GANDUJE A MATSAYIN BABBAN UBA A ƘUNGIYAR

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Yau Juma’a 25 ga watan Octoba, 2019.
Haɗakar fulani makiyaya daga Nahiyar Turai da ƙasar Amurka waɗanda tushiyarsu ta ke a Nahiyar Afrika, sun zaɓi mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin babban uba ga ƙungiyar, tayadda kuma ya zamto ɗan Afrika na farko da ya ya taɓa samun wannan matsayi a ƙungiyar.

Ƙarƙashin ƙungiyar ta fulani maƙiyaya ta Nahiyar Afrika kan zaman lafiya da samar da cigaba, ofishinsu mai lamba 12121, kan titin Audia kusa da gini mai lamba 2308, Dallas Tx 75243, a ƙasar Amurka. Sai kuma ofishinsu mai lamba, 4 Sambo Close, Badiko Jihar Kaduna a Nageriya.

Ƙungiyar ta kuma yabawa mai girma gwamna kan yadda ya ke maida hankali wajen kyautata rayuwar Fulani makiyaya a ƙasashen Nahiyar Afrika gaba ɗaya.

A wasiƙar da su ka aikewa mai girma gwamna mai ɗauke da sa hannun babban sakataren ƙungiyar, Muhammad Farouƙ Auwalu, kan shaida masa wannan zaɓa tasa da su ka yi, sun yi bayani cewa:

“mai girma gwamna, ƙoƙarin da ka ke a gwamnatinka, domin kyautata rayuwar fulani makiyaya a Nageriya, ba shakka ka cancanci yabo daga wannan ƙungiya tamu, saboda waɗannan dalilai, mu ka ga dacewar mu nemi ka zama babban uba ga wannan ƙungiya”.

Dangane da ƙoƙarin mai girma gwamna wajen samar da Rugar zamani ga fulani makiyaya, ƙungiyar ta buƙaci samun damar ganawa da shi mai girma gwamna domin tattauna “muhimman batutuwa, masu alaƙa da fulani makiyaya da kuma sabon tsarin da za a tunƙara wanda zai wanzu ya kuma gamsar da su (Fulanin)”.

Sannan su ka yi ƙarin bayani da cewa a mtsayinsu na ƙungiya za su yi duk mai yiyuwa wajen samar da mafita kan zirga-zirgar fulani makiyaya a Nahiyar Afrika. Kuma za su ba da shawarwari kan yadda za a riƙa alkintawa Fulani makiyaya wurin kiwo a Nageriya da ma Afrika gaba ɗaya.

Daga nan kuma sai su ka labartawa mai girma gwamna yadda haɗakar aiki tare za ta taimaka da kuma yadda su ke da ƙarfin gwiwa cikin fatan ya amince da wannan buƙata tasu a gare shi.

“Ƙungiyarmu ta Fulani makiyaya ta Nahiyar Afrika kan zaman lafiya da samar da cigaba, mu na zaɓar mutum ne mai nagarta da daraja wanda ya ke shimfiɗa shugabnci nagari ga fulani makiyaya a Nahiyar Afrika kowane lokaci. Wanda kuma ya ke ƙoƙari da fafutuka a kansu”.

“Mai girma gwamna, kasancewarka babban uba ga wannan ƙungiya, zai taimaka mana matuƙa wajen samun nasarar cimma manufofi da muradan wannan ƙungiya kan fafutukar kare haƙƙin fulani makiyaya a Nahiyar Afrika.

Inda kuma su ka ƙara da cewa: “wannan zai samu ne ta hanyar ƙara samar da haɗin kai da sauran gwamnonin Arewa da sassan hukumomin samar da cigaba na Duniya da kuma dukkan masu ruwa da tsaki kan wannan gwagwarmaya. Mu na cike da fatan mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai samar da kykkyawan jagorancin da ake buƙata wajen cimma manufofi da muradan da wannan ƙungiya ta sanya a gaba.

Continue Reading

Nasarorin Ganduje

Kano9: Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin bincike kan satar yaran Kano

Published

on

By

GWAMNA GANDUJE YA ƘAFA KWAMITI MAI ƘARFI DOMIN GUDANAR DA BINCIKEN ƘWAƘWAF KAN BADAƘALAR SATAR YARA A JIHAR KANO

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Gwamna Ganduje Ya Kuma Umarci Kwamitin Da Ya Kawo Cikakken Rahoton Mutanen Da Aka Rasa Tun Daga Shekarar (2010) Zuwa Yau (2019) A Jihar Kano.

Yau Juma’a, 25 ga watan Octoba, 2019.
A wani mataki na ƙoƙarin bin haƙƙoƙin yara (9) da aka ceto bayan an yi garkuwa da su an kai su Jihar Anambara, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi domin gudanar da binciken ƙwaƙwaf a ƙarƙashin jagorancin tsohon mai shari’a Wada Umar Rano, kuma mai girma gwamna zai ƙaddamar da kwamitin a ƙarshen wannan wata ranar Alhamis, 31 ga watan Octoba, 2019.

Daga cikin ayyukan da kwamitin zai gudanar, sun haɗa da: bincike mai zurfi kan adadin mutanen da aka rasa daga shekarar (2010) zuwa yau a Jihar Kano tare da gabatar da dukkan hujjoji sahihai rubutattu ko na fatar baka da dukkan wani mutum da za a iya ganewa a matsayin hujja inda yiyuwar hakan.

Daga cikin hujjojin da kwamotin zai yi la’akari da su har da gayyato duk wani mutum a Nageriya da ke da wata hujja ya halarci duk wani taro da membobin kwamitin ya gabatar da hujja ko ya miƙa duk wasu rubutattun bayanai ko duk wata alama ko abubuwa na hujja (a rubuce ko da baki) a mtsayin duk wata hujja da zai iya rantsewa akai ingantacciya ce.

Sauran hanyoyin da za su yi la’kari da su wajen tattara hujjojin har ganawa ko tattaunawa da wani mutum ko wasu mutane ko ƴan jarida domin samar da kammalallu kuma ingantattun bayanai kan mutanen da aka rasa a Jihar Kano daga wancan lokaci da aka bayyana zuwa yau.

Bayan sun kammala tattara bayanan kan yawan mutanen da aka rasa da kuma dalilan da ke haifar da hakan, kai tsaye kwamitin zai miƙa rubutaccen rahoton sakamakon bincikensa ga gwamnatin Jihar Kano.

Idan dai za a iya tunawa a kwana-kwanannan rundunar ƴan sanda ta ƙasa shiyar Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin amintaccen shugaban rundunar (CP) Ahmed Iliyasu ba ta kai ga kammala warware matsalolin yaran da aka sace a Jihar Kano ba.

Jimillar yaran su tara ƴan shekaru 2 zuwa 10 da aka yi garkuwa da su, 8 daga cikinsu an sayar da su ne a Farawa da ke Jihar Anambara. Wasu daga cikin waɗanda iftila’in ya afkawa sun kasance ne a matsayin bayi fiye da tsawon shekaru biyar a Jihar ta Anambara inda aka sauya musu yanayinsu na ainahi.

Sashe na biyu na doka kan kwamitin binciken cikin baka ta (CAP.29) a dokokin Jihar Kano na (1990) ya ba wa mai girma gwamna cikakkiyar dama da ikon kafa wannan kwamiti na bincike.

Dangane da wannan batu, gwamna Ganduje ya byyana cewa: “a hukumance mu na sanar da al’umma membobin wannan kwamiti gaba ɗaya nauyin da mu ka ɗora musu na gudanar da bincike mai zurfi kan matsalar ɓatan al’umma a Jihar Kano daga shekarar (2010) zuwa (2019) da su ka shafi 30 ga watan Octoba, 2019 da kuma 30 ga watan Nuwamban 2019”.

Da ya ke bayyana farin cikinsa kan yara taran da aka gano aka kuma miƙa su ga iyayensu, ya bayyana cewa gwamnatinsa “za ta cigaba da tunkarar wannan barazana ta tsaro da muhimmanci domin daƙile ta gaba ɗaya”.

Kuma Kwamitin zai saurari ɓangaren waɗanda matsalar ta shafa domin tattara hujjoji na baki da kuma rubutattu. Sannan kuma za su duba yiyuwar ziyartar wurin da lamarin ya faru, sannan gwamnati za ta tabbatar da ta yi duk mai iyuwa wajen magance dukkan ire-iren waɗannan matsaloli.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending