Connect with us

Labarai

Gwamna Ganduje ya kaddamar da fara rijistar Fasfo na zamani a Kano

Published

on

GWAMNA GANDUJE YA ƘADDAMAR DA FARA AIKIN RIJITAR SABON FASFO IRIN NA ZAMANI A JIHAR KANO

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Gwamna Ganduje, Ya Yaba Kan Yadda AKa Yi Amfani Da Sabuwar Fasahar Zamani Wajen Binciken Ƴan Ƙasashen Ƙetare Masu Haurowa Zuwa Nageriya.

-Shugaban Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙasa, Babandede,Ya Yaba Kan Yadda Jihar Kano Ta Kasance Cikin Aminci Da Zama Lafiya.

Yau Talata, 29 ga watan Octoba, 2019.
A ya yin da ya ke yabawa hukumar shige da fice ta ƙasa kan amfani da sabuwar fasahar zamani wacce za ta taimaka wajen gano yawan baƙi ƴan ƙasashen waje waɗanda ke haurowa Nageriya ba bisa ƙa’ida ba, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana wannan sabon yunƙuri a matsayin “wata hanya ta kimiyya wacce za ta taimaka wajen kare ƙasarmu. Sannan kuma a lokaci guda na zama wani tsari na musamman wanda zai taimaka wajen tabbatar da kariya ga ƴan ƙasa da kuma baƙin gaba ɗaya.

Gwamna Ganduje ya yi ƙarin bayani da cewa: “Mu na da buƙatar mu zama masu amfani da kimiyya cikin rayuwarmu, musamman ma a kan sha’anin tsaro. Wannan ya shaida mana ƙarara yadda hukumar shige da fice ta ƙasa ta kai mu zuwa ga mataki nagaba a ƙarƙashin shugabancin Muhammad Babandede”.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a ya yin da ya ke ƙaddamar da fara aikin rijistar sabon kati (Fasfo) irin na zamani wanda ke tabbatar da shaidar zaman mutum cikakken ɗan (Nageriya) da kuma ba shi damar yin zirga-zirga zuwa ƙasashen ƙetare wanda aka gudanar a harabar makarantar horar da jami’an hukumar shige da fice ta ƙasa (Immigration Training School) da ke Jihar Kano.

Aikin wanda ya ke ƙunshe da manufar samar da wata babbar dama kan sha’anin tsaro, wacce za ta samar da wata ingantacciyar cibiya kan bibiyar dukkan wasu baƙi da aka yi wa rijista ƴan ƙasashen waje da ke Nageriya.

Gwamna Ganduje ya kuma ƙara da cewa: “a yanayin ɗabi’ar baƙi na Kano, za ta ba su damar maida hankali matuƙa kan yawan baƙin da ba ƴan asalin ƙasa ba ne, kamar yadda ya ke cewa: “ya zama wajibi a maida hankali yadda ya kamata. Ina mai jan hankali da kira ga dukkan waɗanda ba ƴan ƙasa ba ne da su hanzarta zuwa a yi musu rijista”.

Daga nan kuma sai gwamna Ganduje ya ƙara bayyana hasashensa da cewa, samun cikakken bayani game da adadin yawan baƙi ƴan ƙasashen waje, wata tabbatacciyar hanya ce wacce za ta taimaka wajen kare Jiha da ƙasa gaba ɗaya. Inda ya kuma ƙara tunasar da cewa Jihar Kano ta kasance cikin zama ne irin na da a yammacin nahiyar Afrika. Daga nan kuma sai ya ƙara da ba da tabbacin Jihar wajen ba da dukkan haɗin kai da kuma goyon bayan da ake da buƙata waje samun nasarar wannan sabon tsari.

“Mu na cikin farin ciki tare da alfahari da shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa, Muhammad Babandede kan wannan sabon tsari da ya samar ƙarƙashin ɗaukar nauyin hukumar. Wannan yunƙuri ne na kishin ƙasa da kuma ƙarfafa gwiwar kowane sashe”. Inji Gwamna Ganduje.

Tunda farko a nasa jawabin, shugaban hukumar shige da ficen ta ƙasa (NIS), Mallam Muhammad Babandede wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar na Jihar Kano, Mallam Dikko Nuhu Yashe, ya yi tsokaci da cewa: “Babban dalilin ƙirƙiro da wannan sabon tsari shi ne batun samar da tsaro da kuma samar da wata cibiya ko matattara wadda za ta taimakawa hukumar wajen bibiya da shawo kai da kuma sanin dukkan wani motsi da shige da ficen mutanen da ba ƴan ƙasa (Nageriya) ba ne”.

Daga nan sai kuma ya ƙara da cewa: “wannan aiki ne da ya shafi dukkan mutanen da ba ƴan asalin Nageriya ba ne, walau masu zaman dindindin ko na wucin gadi, dan haka akwai buƙatar gaba ɗaya su zo su gabatar da kansu ga wannan aiki wanda za a gudanar kyauta ba tare da karɓar ko sisin kwabo ba”.

Bayan nan kuma, sai ya godewa gwamna Ganduje kan cikakken haɗin kan da ya ke ba wa hukumar kan dukkan ayyukan da ta sako a gaba, kamar yadda ya ke cewa: “Mun yaba da irin goyon baya da gudunmawar da gwamnatin Jiha ta ke ba wa wannan hukuma tamu da kuma yabo na musamman ga mai girma gwamna da ya kasance a wannan muhimmin taro.

A ya yin da ya ke kira ga mai girma gwamna da ya yi kira da babbar murya ga dukkan mutanen da ba ƴan asalin Nageriya ba a Jihar Kano don ganin sun ɗauki wannan aiki da muhimmanci, ya bayyana cewa: “su yi la’akari da cewa tsari ne da manufa ta gwamnatin tarayya wajen gudanar da wannan al’amari”.

Haka zalika, gwamna Ganduje ya ziyarci ofishin hukumar na yin rijistar Fasfo ɗin da ke kasuwar (Farm Centre) inda ya cika dukkan sharuɗan yin rijistar aka ba shi sabon katin Fasfo ɗin na zamani wanda ya ke da wa’adin shekaru (10) kafin sake sabunta shi.

Inda kuma gwamna Ganduje ya ba da ƙwarin gwiwa da cewa, sabon Fasfo ɗin na zamani, wata bayyananniyar hujja ce da ke nuna namijin ƙoƙari daga ɓangren shugabancin hukumar ta shige da fice. Inda ya kuma ƙara da bayyana hakan a matsayin cigaba da samun nasara a ɗaukacin fannin sha’anin tsaro zuwa gaba, tare da buga misali cewa “tundaga hanyoyin da na bi wajen mallakar wannan sabon Fasfo, na fahimci lallai cigaban zamani ya samu kamar yadda ake yi a Duniya”.

Babandede ta bakin wakilinsa, mataimakinsa Mista, Tamprica V. Oyedeji, ya yi tsokaci da cewa : “shekaru goma bayan bayyana batun wannan sabon tsarin fasfo, hukumar a shekarar (2017) ya yin taron shekara na shugaban hukumar a birnin Abekuta na Jihar Ogun, ta sadaukar da bibiyar takardu kan tsarin ƙungiyoyin sufuri masu zaman kansu na Duniya domin kyautata tsaro kan takardun a zamanance kamar yadda ake yi a Duniya”.

Inda ya kuma ƙara da cewa : “samar da wannan sabon tsari manufa ce mai alaƙa da tsaron ƙasa da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci, shi ya sa ma tsarin ke kunshe da matakai kusan guda (25) ciki har da batun shigar da nombobin katin shaidar zama ɗan ƙasa (NI. NO.).

Daga ƙarshe sai ya kuma ƙarƙare da cewa : “Ranka ya daɗe mai girma gwamna, a madadin shugaban hukumar na ƙasa gaba ɗaya, Mallam Muhammad Babandede da ofishinsa da ɗaukacin jami’an hukumar ta shige da fice, ina farin cikin sanar da Jiha cewa za mu cigaba da ba da himma wajen kare al’ummar Jihar Kano da na Nageriya gaba ɗaya. Za mu cigaba da yin aiki tare da gwamnatin Jihar Kano domin samun kykkyawar nasara”.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Majalissar Zartarwa Ta Amince  A Kafa Ƙarin Masarautu Guda Huɗu U A Jihar Kano 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Kuma Tuni Ta Tura Ƙudirin Dokar Zuwa Gaban Zauren Majalissar Dokoki Na Jihar Kano.

Yau Litinin, 2 ga watan Disamba, 2019.
A wani zama da ta gudanar a daren Jiya Lahadi, majalissar zartarwa ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da ƙudirin dokar kafa ƙarin masarautu guda huɗu a Jihar Kano. Waɗanda su ka haɗa da masarautar: Bichi da Gaya da Rano da kuma Ƙaraye. Inda tuni kuma majalissar ta tura ƙudirin dokar zuwa gaban zauren majalissar dokoki na Jiha.

Sanarwar da aka fitar daga gidan gwamnati, ta kuma ƙara yin bayani da cewa dama can akwai wasu daga cikin waɗannan masarautu tun shekarun baya masu tsawo da su ka wuce, juyin zamani ne ya nemi ya shafe tarihinsu, kuma ko a zamanin janhoriya ta biyu sai da aka nemi a farfaɗo da su, amma aka samu tsaiko.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa majalissar zartarwa ta tattauna sosai game da alfanun ƙarin nasarautun kafin ta cimma wannan matsaya da ta ɗauka, ta kuma fahimci cewa ƙarin masarautun zai taimaka sosai wajen ƙara kusanci a tsakanin al’umma da sarakunan gargajiya. Sannan kuma ƙarin masarautun zai taimaka matuƙa wajen ƙara haɓaka harkokin kasuwanci da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Kano cikin hanzari.

Haka zalika, ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na ilimi kyauta kuma wajibi tun daga firamare har zuwa babbar sakandire, ya na buƙatar taka rawar al’umma sosai da sosai musamman ma sarakunan gargajiya domin samun nasarar shirin. Dan haka ƙarin masarautun zai taimaka sosai da sosai wajen cimma wannan buri.

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa ƙudirin dokar da aka ɗabbaka a zauren majalissaar dokoki a 2019, kotu ta rushe shi ne saboda mutum ne daga cikin al’umma ya gabatar da shi ba ɗaya daga cikin ƴan majalissa ba.

Kamar yadda sanarwar ta ƙara, majalissar zartarwar ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta kuma buƙaci zauren majalissar dokokin na Jihar Kano da su yi duba da buƙatun al’umma wajen amincewa da ƙudirin dokar.

Continue Reading

Labarai

Gwamna Ganduje Ya Taya Mallam Ibrahim Shekarau Murnar Samun Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-“Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa Da Aka Ba Wa Sanata Shekarau Alama Ce Da Ke Ƙara Shaida Yadda Duniyar Ilimi Ta Gamsu Da Irin Ɗumbin Gudunmawar Da Ya Ba Ta A Zamanin Da Ya Riƙe Matsayin Gwamna Da Muƙamin Ministan Ilimi Na Nageriya”. Inji Gwamna Ganduje.

Yau Asabar, 30 ga watan Nobemba, 2019.
Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano hawa biyu, kana kuma sanata mai ci, Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano murnar samun lambar yabo ta digirin girmamawa wanda Jami’ar Ritman da ke birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom ta ba shi a wannan rana ta Asabar.

Digirin girmamawar wacce jami’ar ta ba shi saboda irin ɗumbin gudunmawar da ya bayar a fannin iilimi a zamanin ya na matsayin gwamna da matsayin ministan ilimi, gwamna Ganduje ya taya shi murna a madadin gwamnatin Jihar Kano da al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya.

Kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar taya murnar da gwamna Ganduje ya bayar, “mai girma gwamna ya ga lambar yabo ta digirin girmamawa da aka ba wa Sanata Ibrahim Shekaru, inda lambar ke ƙara shaida yadda fannin ilimi ya gamsu da irin ɗumbin nasarori da gudunmawar da ya bayar a fannin da kuma gina rayuwar ɗan adam a lokacin da ya riƙe matsayin gwamna da kuma Ministan Ilimi a Nageriya.

Idan za a iya tunawa, ko a shekarar 2009, Sanata Shekarau ya samu irin wannan lambar yabo ta digirin girmamawa daga Jami’ar ƙasa ta Nsuka”. Sanarwar ta bayyana.

Inda kuma gwamna Ganduje ya ƙara da cewa wannan lambar yabo ga sanata Shekarau tambar ƙara zaburar da shi ne ya ƙara himma da ƙoƙari kan ƙoƙarin da ya ke na ba da gudunmawa wajen gina ƙasa da kuma gina rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Ya yin da ya ke taya Sanata Shekarau murnar wannan ƙarin matsayi da ya samu, gwamna Ganduje ya yi masa fatan alkhairi tare da fatan ya ƙara cigaba da dagewa wajen ba da gudunmawa kan cigaban ƙasa da sauran jama’a.

Continue Reading

Labarai

JAMI’AN TSARO SUN SAMU NASARAR KAME WANDA YA SHIRYA AURAR DA FATIMA GANDUJE TA BOGI

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ya Samar Da Fatima Ganduje Ta Bogi Ya Karɓi Kuɗi Kimanin Naira Miliyan Biyar Da Sunan Zai Ba Da Auren Fatima Ganduje Ta Gaske.

-Iyalan Gwamna Ganduje Sun Ba Da Umarni Jami’an Tsaro Su Cafke Duk Wani Ko Wata Da Za Su Bayyana Kansu A Matsayin Yaran Gidan Su Damfari Al’umma.

Yau Asabar, 23 ga watan Nobemba, 2019.
Jami’an tsaro sun samu nasarar kame wani matashi mai suna Abdullahi Zakari, wanda ya bayyana kansa a matsayin yaron gidan mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya damfari wani mutum mai sana’ar saida magunguna mai suna Alhaji Bashir Amadu Usaini da ke unguwar Tudun Yola zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan Biyar da sunan wai zai haɗa shi da ƴar mai girma gwamna Fatima Ganduje ya aura.

Yadda lamarin ya faru shi ne: tun kafin Fatima Ganduje ta yi aure, Abdullahi Zakari ya samu wani mai suna Alhaji Bashir Amadu ya kwaɗaita masa cewar shi yaron gidan gwamna Ganduje ne, dan haka ya yi masa alƙawarin zai haɗa shi aure da Fatima Ganduje. Sannu a hankali har ta kai ga wannan ɗan damfara (Abdullahi Zakari) ya samar da Fatima Ganduje ta ƙarya ya haɗa su da Alhaji Bashir Amadu su na waya da juna da sunan soyayya.

Sannu-sannu har ta kai ga wannan Fatima ta bogi ta na neman kuɗi a wurin Alhaji Bashir Amadu inda ta ke shaida masa cewar wai auren dole za a yi mata a gida, dan haka ba ta tambayar kowa kuɗi in ba shi ba, saboda shi ta ke so ta aura.

Sannan kuma, shi wannan ɗan damfara ya samar da wata matar ta bogi a matsayin Balaraba Ganduje, wato yayar Fatima Ganduje, ta yadda duk kuɗin da Fatima Ganduje ta bogi za ta nema a wurin Alhaji Bashir Amadu, ita wannan Balaraba Ganduje ta bogin ce ta ke ƙara ba shi tabbacin da ƙarfin gwiwa kan ya ba da ko nawa ne ta tambaye shi saboda wai ita Fatiman ba ta tambayar kowa kuɗi a gidan nasu sai shi saboda shi ne ta ke son zai aure ta, wanda hakan ne kuma ya ke sanya shi ko da yaƙi ko kuma ba shi da kuɗi a lokacin to wannan ƙaimi da Balaraba Ganduje ta bogin ta ke yi masa kan sa shi ya nemo ya bayar.

Bayan haka, shi dai wannan ɗan damfara, har Gwaggo wato Hajiya Gafsat Ganduje ya samar ta bogi, inda ya sanya ita waccar Fatiman bogin ta nemi wayar mahaifiyar shi wanda ake damfara ɗin, Bashir Amadu ta haɗa su da wannan Gwaggo ta bogi su ka gaisa da mahaifiyarsa a lokacin da ba ta da lafiya.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da Fatima Ganduje da Balaraba Ganduje da kuma (Gwaggo) Hafsat Ganduje duk na bogi kafin Fatima Ganduje ta gaske ta yi aure har tsawon kusan shekaru uku.

Sannan bayan Fatima Ganduje ta gasken ta yi aure, duk da haka ba su ƙyale shi ba, wannan Fatima Ganduje ta bogin ta cigaba da yi masa waya ta na faɗa masa cewar ita fa ba zaman auren nan za ta yi ba domin dole aka yi mata dan haka za ta kashe auren ta fito ta aure shi.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da waɗannan mata a matsayin ƴaƴa ne na gwamna, wato Fatima da Balaraba, da kuma mahaifiyarsu Gwaggo ya yi ta karɓan kuɗi a hannun wannan bawan Allah mai suna Bashir Amadu Usaini har kimanin Naira Miliyan Biyar cikin shekaru uku da su ka shafe.

Sai dai jami’in tsaro sun samu nasarar kame wannan ɗan damfara, har ma an gurfanar da shi a gaban kotun Noman Salak da ke nan Jihar Kano a jiya, kuma alƙali ya tura shi zaman gidan kaso kafin a nemo sauran matan da ya yi amfani da su wajen shirya wannan damfara da zamba a dawo a cigaba da shari’ar.

Sannan kuma tuni iyalan mai girma gwamna sun ba da gargaɗi kan a guji yarda da duk wani wanda zai je wa da wani da irin wannan alaƙa, sannan kuma duk wanda aka kama to ayi gaggawar sanar da jami’an tsaro mafi kusa domin su kame shi.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending