Connect with us

Labarai

Gwamna Ganduje zai kara karfafa hurdar jihar Kano da kasar Faransa

Published

on

GWAMNA GANDUJE ZAI ƘARA ƘARFAFA DANGANTAKAR HULƊAR KASUWANCI DA AL’ADU A TSAKANIN JIHAR KANO DA KUMA ƘASAR FARANSA

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ƙasar Faransa Ta Shiryawa Gwamna Ganduje Taron Tattaunawa A Tsakaninsa Da Bankin Haɓaka Tattalin Arziƙi Na Ƙasar Faransa Domin Kawo Cigaba Jihar Kano.

-Jakadan Ƙasar Faransa A Nageriya, Ya Yabawa Ƙoƙarin Gwamna Ganduje Wajen Kyautata Fannin Ilimi Da Sauran Fannoni A Gwamnatinsa.

Yau Talata, 22 ga watan Octoba, 2019.
A ƙoƙarinsa na cigaba da haɓaka tattalin arziƙin Jiha da kuma cigaba da kyautata dangantakar tattalin arziƙi da sauran ƙasashen Duniya, an tsara mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai kai wata ziyarar aiki zuwa ƙasar Faransa inda zai gana da manyan ƴan kasuwa na ƙasar domin jawo hankalin masu zuba jari wajen ƙara ƙarfafa dangantakar tattalin arziƙi da ta al’adu a tsakanin Jihar Kano da kuma ƙasar ta Faransa.

Daga cikin ginshiƙan ziyarar tasa, har da batun ganawa ta musamman tare da ɗalibai ƴan asalin Jihar Kano waɗanda su ke karatu a ƙasar ta Faransa a cikin jami’o’i daban-daban na ƙasar inda wasu su ke matakin digiri na biyu wasu kuma su na matakin digirin-digirgir.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a ya yin da ya ziyarci ofishin jakadancin Faransa da ke Abuja inda ya gana da jakadan ƙasar Mista Jeremo Pasquier a wannan rana ta Talata, inda kuma ya ba shi tabbacin yin iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya samo gagarumar nasara kan tattalin arziƙin Jihar Kano wajen ganawa da manyan ƴan kasuwa na ƙasar ta Faransa dazarar ya je.

A wannan zango mulki nasa na biyu, gwamna Ganduje ya bayyana cewa zai yi aiki tuƙuru wajen ganin jihar Kano ta zama mashigar ƴan kasuwa na duniya masu zuba jari. “A yunƙurinmu na kyautata tattalin arziƙin Jiharmu, za mu cigaba da haɗa hannunmu da sauran ƙasashen duniya kamar Faransa kan tattalin arziƙi da kuma al’adu”. Inji Gwamna Ganduje.

Dangane da kyautata dangantakar al’adu, a cewar gwamna Ganduje, a lokaci guda, zai zama wata hanya ta ƙara kyautata sha’anin tsaro da kuma zaman lafiya a Duniya, inda ya yi ƙarin bayani da cewa: “Tare da daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin Jihar Kano da ƙasar Faransa, ziyarata zuwa ƙasar za ta zama wata babbar dama ce ta ƙara ƙarfafa dangantakar wacce za ta kasance har abada”. Cewar Gwamna Ganduje.

“Sannan zan yi amfani da wanna dama wajen yin godiya ga ƙasar Faransa dangane da damar tallafin karatu da ku ka ba wa matasanmu da kuma malamanmu na manyan makarantun gaba da sakandire”. Inji gwamna Ganduje.

Inda daga nan kuma gwamna Ganduje ya ƙara da cewa ganawar da zai yi da ɗalibai ƴan asalin jihar Kano da ke karatu a ƙasar ta Faransa, zai taimaka wajen ƙara sanyawa ɗaliban ƙarsashi da himmar cigaba da maida hankali kan karatunsu.

Daɗi da ƙari, gwamna Ganduje zai yi amfani da ziyarar wajen gabatarwa da ƙasar ta Faransa halin da ake ciki dangane da gudunmawar kuɗaɗe da ta ba wa Jihar Kano a baya domin inganta fannin samar da ruwan sha a Jihar Kano.

Kamar yadda ya bayyana, “mun yi amfani da damar wajen kyautata aikin samar da ruwa, wadda kuma babu wata gagarumar matsala tun (1928) lokacin da aka ƙirƙiro ta har zuwa yau. Wannan kyautatawa da mu ka samu daga gwamnatin Faransa ta zama wani abin alfahari a gare mu”.

Bayan gyara aikin samar da ruwan sha, gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin Jiha ta ƙara ƙaimi wajen ƙara kyautata hanyoyin samar da ruwan, inda ya yi ƙarin haske da cewa: “mu na yin duk mai iyuwa iya bakin ƙoƙarinmu domin ganin cewar mun kyautata sha’anin samar da ruwan sha kamar yadda mu ka fara cikin juriya da jajircewa”. Gwamna Ganduje ya bayyana.

“Ina mai farin cikin shaida muku cewa, mu na gudanar da gagarumin aiki da kyautatawa a fannin samar da ruwan sha. Kamar yadda mu ke yi a sauran fannoni a Jihar Kano”. Inji Gwamna Ganduje.

A ya yin da ya ke maida jawabi, jakadan ƙasar ta Faransa a Nageriya, Mista, Pasquer, ya yabawa gwamna Ganduje kan yadda ya ke kykkyawan aiki tuƙuru a fannin ilimi da kuma sauran fannoni a gwamnatinsa.

Daga nan kuma sai ya ƙara da ba da tabbacin ƙasarsu ta Faransa wajen cigaba da marawa gwamnatin Jihar Kano baya kan fannin ilimi da kuma tabbatar da kykkyawar alaƙar dangantakar tattalin arziƙi a tsakanin ƙasar da kuma Jihar Kano.

A ƙoƙarin kyautata dangantakar tattalin arziƙin daga dukkan sasannin cigaba, Jakada Pasquier ya bayyana cewa, “akwai shiri da aka yi inda mai girma gwamna zai gana da bankin haɓaka tattalin arziƙi na ƙasar Faransa da zarar ya samu isa can. Wannan zai ɗauke mu hanya mai tsawo wajen kyautata alaƙar dangantakarmu”.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Majalissar Zartarwa Ta Amince  A Kafa Ƙarin Masarautu Guda Huɗu U A Jihar Kano 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Kuma Tuni Ta Tura Ƙudirin Dokar Zuwa Gaban Zauren Majalissar Dokoki Na Jihar Kano.

Yau Litinin, 2 ga watan Disamba, 2019.
A wani zama da ta gudanar a daren Jiya Lahadi, majalissar zartarwa ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da ƙudirin dokar kafa ƙarin masarautu guda huɗu a Jihar Kano. Waɗanda su ka haɗa da masarautar: Bichi da Gaya da Rano da kuma Ƙaraye. Inda tuni kuma majalissar ta tura ƙudirin dokar zuwa gaban zauren majalissar dokoki na Jiha.

Sanarwar da aka fitar daga gidan gwamnati, ta kuma ƙara yin bayani da cewa dama can akwai wasu daga cikin waɗannan masarautu tun shekarun baya masu tsawo da su ka wuce, juyin zamani ne ya nemi ya shafe tarihinsu, kuma ko a zamanin janhoriya ta biyu sai da aka nemi a farfaɗo da su, amma aka samu tsaiko.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa majalissar zartarwa ta tattauna sosai game da alfanun ƙarin nasarautun kafin ta cimma wannan matsaya da ta ɗauka, ta kuma fahimci cewa ƙarin masarautun zai taimaka sosai wajen ƙara kusanci a tsakanin al’umma da sarakunan gargajiya. Sannan kuma ƙarin masarautun zai taimaka matuƙa wajen ƙara haɓaka harkokin kasuwanci da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Kano cikin hanzari.

Haka zalika, ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na ilimi kyauta kuma wajibi tun daga firamare har zuwa babbar sakandire, ya na buƙatar taka rawar al’umma sosai da sosai musamman ma sarakunan gargajiya domin samun nasarar shirin. Dan haka ƙarin masarautun zai taimaka sosai da sosai wajen cimma wannan buri.

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa ƙudirin dokar da aka ɗabbaka a zauren majalissaar dokoki a 2019, kotu ta rushe shi ne saboda mutum ne daga cikin al’umma ya gabatar da shi ba ɗaya daga cikin ƴan majalissa ba.

Kamar yadda sanarwar ta ƙara, majalissar zartarwar ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta kuma buƙaci zauren majalissar dokokin na Jihar Kano da su yi duba da buƙatun al’umma wajen amincewa da ƙudirin dokar.

Continue Reading

Labarai

Gwamna Ganduje Ya Taya Mallam Ibrahim Shekarau Murnar Samun Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-“Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa Da Aka Ba Wa Sanata Shekarau Alama Ce Da Ke Ƙara Shaida Yadda Duniyar Ilimi Ta Gamsu Da Irin Ɗumbin Gudunmawar Da Ya Ba Ta A Zamanin Da Ya Riƙe Matsayin Gwamna Da Muƙamin Ministan Ilimi Na Nageriya”. Inji Gwamna Ganduje.

Yau Asabar, 30 ga watan Nobemba, 2019.
Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano hawa biyu, kana kuma sanata mai ci, Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano murnar samun lambar yabo ta digirin girmamawa wanda Jami’ar Ritman da ke birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom ta ba shi a wannan rana ta Asabar.

Digirin girmamawar wacce jami’ar ta ba shi saboda irin ɗumbin gudunmawar da ya bayar a fannin iilimi a zamanin ya na matsayin gwamna da matsayin ministan ilimi, gwamna Ganduje ya taya shi murna a madadin gwamnatin Jihar Kano da al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya.

Kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar taya murnar da gwamna Ganduje ya bayar, “mai girma gwamna ya ga lambar yabo ta digirin girmamawa da aka ba wa Sanata Ibrahim Shekaru, inda lambar ke ƙara shaida yadda fannin ilimi ya gamsu da irin ɗumbin nasarori da gudunmawar da ya bayar a fannin da kuma gina rayuwar ɗan adam a lokacin da ya riƙe matsayin gwamna da kuma Ministan Ilimi a Nageriya.

Idan za a iya tunawa, ko a shekarar 2009, Sanata Shekarau ya samu irin wannan lambar yabo ta digirin girmamawa daga Jami’ar ƙasa ta Nsuka”. Sanarwar ta bayyana.

Inda kuma gwamna Ganduje ya ƙara da cewa wannan lambar yabo ga sanata Shekarau tambar ƙara zaburar da shi ne ya ƙara himma da ƙoƙari kan ƙoƙarin da ya ke na ba da gudunmawa wajen gina ƙasa da kuma gina rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Ya yin da ya ke taya Sanata Shekarau murnar wannan ƙarin matsayi da ya samu, gwamna Ganduje ya yi masa fatan alkhairi tare da fatan ya ƙara cigaba da dagewa wajen ba da gudunmawa kan cigaban ƙasa da sauran jama’a.

Continue Reading

Labarai

JAMI’AN TSARO SUN SAMU NASARAR KAME WANDA YA SHIRYA AURAR DA FATIMA GANDUJE TA BOGI

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ya Samar Da Fatima Ganduje Ta Bogi Ya Karɓi Kuɗi Kimanin Naira Miliyan Biyar Da Sunan Zai Ba Da Auren Fatima Ganduje Ta Gaske.

-Iyalan Gwamna Ganduje Sun Ba Da Umarni Jami’an Tsaro Su Cafke Duk Wani Ko Wata Da Za Su Bayyana Kansu A Matsayin Yaran Gidan Su Damfari Al’umma.

Yau Asabar, 23 ga watan Nobemba, 2019.
Jami’an tsaro sun samu nasarar kame wani matashi mai suna Abdullahi Zakari, wanda ya bayyana kansa a matsayin yaron gidan mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya damfari wani mutum mai sana’ar saida magunguna mai suna Alhaji Bashir Amadu Usaini da ke unguwar Tudun Yola zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan Biyar da sunan wai zai haɗa shi da ƴar mai girma gwamna Fatima Ganduje ya aura.

Yadda lamarin ya faru shi ne: tun kafin Fatima Ganduje ta yi aure, Abdullahi Zakari ya samu wani mai suna Alhaji Bashir Amadu ya kwaɗaita masa cewar shi yaron gidan gwamna Ganduje ne, dan haka ya yi masa alƙawarin zai haɗa shi aure da Fatima Ganduje. Sannu a hankali har ta kai ga wannan ɗan damfara (Abdullahi Zakari) ya samar da Fatima Ganduje ta ƙarya ya haɗa su da Alhaji Bashir Amadu su na waya da juna da sunan soyayya.

Sannu-sannu har ta kai ga wannan Fatima ta bogi ta na neman kuɗi a wurin Alhaji Bashir Amadu inda ta ke shaida masa cewar wai auren dole za a yi mata a gida, dan haka ba ta tambayar kowa kuɗi in ba shi ba, saboda shi ta ke so ta aura.

Sannan kuma, shi wannan ɗan damfara ya samar da wata matar ta bogi a matsayin Balaraba Ganduje, wato yayar Fatima Ganduje, ta yadda duk kuɗin da Fatima Ganduje ta bogi za ta nema a wurin Alhaji Bashir Amadu, ita wannan Balaraba Ganduje ta bogin ce ta ke ƙara ba shi tabbacin da ƙarfin gwiwa kan ya ba da ko nawa ne ta tambaye shi saboda wai ita Fatiman ba ta tambayar kowa kuɗi a gidan nasu sai shi saboda shi ne ta ke son zai aure ta, wanda hakan ne kuma ya ke sanya shi ko da yaƙi ko kuma ba shi da kuɗi a lokacin to wannan ƙaimi da Balaraba Ganduje ta bogin ta ke yi masa kan sa shi ya nemo ya bayar.

Bayan haka, shi dai wannan ɗan damfara, har Gwaggo wato Hajiya Gafsat Ganduje ya samar ta bogi, inda ya sanya ita waccar Fatiman bogin ta nemi wayar mahaifiyar shi wanda ake damfara ɗin, Bashir Amadu ta haɗa su da wannan Gwaggo ta bogi su ka gaisa da mahaifiyarsa a lokacin da ba ta da lafiya.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da Fatima Ganduje da Balaraba Ganduje da kuma (Gwaggo) Hafsat Ganduje duk na bogi kafin Fatima Ganduje ta gaske ta yi aure har tsawon kusan shekaru uku.

Sannan bayan Fatima Ganduje ta gasken ta yi aure, duk da haka ba su ƙyale shi ba, wannan Fatima Ganduje ta bogin ta cigaba da yi masa waya ta na faɗa masa cewar ita fa ba zaman auren nan za ta yi ba domin dole aka yi mata dan haka za ta kashe auren ta fito ta aure shi.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da waɗannan mata a matsayin ƴaƴa ne na gwamna, wato Fatima da Balaraba, da kuma mahaifiyarsu Gwaggo ya yi ta karɓan kuɗi a hannun wannan bawan Allah mai suna Bashir Amadu Usaini har kimanin Naira Miliyan Biyar cikin shekaru uku da su ka shafe.

Sai dai jami’in tsaro sun samu nasarar kame wannan ɗan damfara, har ma an gurfanar da shi a gaban kotun Noman Salak da ke nan Jihar Kano a jiya, kuma alƙali ya tura shi zaman gidan kaso kafin a nemo sauran matan da ya yi amfani da su wajen shirya wannan damfara da zamba a dawo a cigaba da shari’ar.

Sannan kuma tuni iyalan mai girma gwamna sun ba da gargaɗi kan a guji yarda da duk wani wanda zai je wa da wani da irin wannan alaƙa, sannan kuma duk wanda aka kama to ayi gaggawar sanar da jami’an tsaro mafi kusa domin su kame shi.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending