Connect with us

Labarai

Kungiyar lauyoyi ta kaiwa gwamna Ganduje ziyara

Published

on

ƘUNGIYAR LAUYOYIN NAGERIYA TA GUDANAR DA TATTAKIN JADDADA GOYON BAYA GA GWAMNA GANDUJE

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ƙungiyar Ta Kuma Yabawa Gwamna Ganduje Kan Ƙoƙarinsa Na Haɓaka Tsaro A Jihar Kano

-Gwamna Ganduje Ya Ba Da Tabbacin Maƙala Na’urar Naɗar Bayanai (CCTV) A Loko Da Saƙo Na Jihar Kano Domin Cigaba Da Inganta Tsaro A Jihar Gaba Ɗaya.

-Sannan Kuma, Gwamna Ganduje Zai Shirya Taro Na Musamman Kan Ƴan Sanda Na Cikin Al’umma

Yau Asabar, 26 ga watan Octoba, 2019.
Ƙwararrun Lauyoyi a Jihar Kano ƙarƙashin ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA), a wannan rana sun ziyarci gidan gwamnatin Jihar Kano domin nuna goyon bayansu da kuma girmamawa ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan yadda ya tunkari ƙalubalen matsalar tsaron Jihar da ya kunno kai a wannan yanayi baya-bayan nan.

Mai girma gwamna ya karɓe su ne a babbar ƙofar shiga gidan gwamnati da ke babban titin Jihar, a ya yin da shugaban ƙungiyar ta Lauyoyin Nageriya (NBA) reshen Jihar Kano, Barista, Musa Abdul Lawan ya gabatar da jawabin ba da tabbacin goyon bayansu da kuma girmamawarsu ga gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamna Ganduje. Inda ya kuma ƙara da cewa: “ba wai reshen Kano ne kaɗai na ƙungiyar ta (NBA) ba, har da reshen ƙaramar hukumar Ungogo su ma mun samu goyon bayansu kan wannan ziyarar girmamawa da nuna goyon baya”.

Kamar yadda shugaban ƙungiyar ya bayyana ƙungiyar ta shirya taro a Jihar dangane da batun ƙalubalen matsalar tsaro da ya kunno kai, “mai girma gwamna dukkan ƙoƙarinka na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano ya gamsar. Mu na ba ka tabbacin kasancewa a bayanka a kowane lokaci domin tabbatar da cewa Jihar Kano ta cigaba da kasancewa cikin aminci”.

Inda ya ƙara bayyana farin cikinsa da cewa “ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kano wajen tabbatar da aminci a Jihar a kowane lokaci za mu cigaba da mara mata baya. Mu na alfaharin cewa Jihar Kano ta na cikin aminci. Allah ya ƙaro alkhairi da cigaba mai girma gwamna”.

A ya yin da ya ke maida jawabi, gwamna Ganduje ya ba su tabbacin gwamnatinsa na cigaba da mutunta doka da oda a kowane lokaci. Tare kuma da ƙara ƙarfafa fannin shari’a da kuma wanzar da kykkyawan jagoranci kan fannin shari’ar Jihar.

Daga nan kuma sai ya ƙara da yin godiya ga wannan ƙungiya ta ƙwararrun lauyoyi kan wannan goyon baya da ƙara ƙarfafa gwiwa da su ka bayyana masa, kamar yadda ya ke cewa “wannan yabo naku gare mu kan kykkyawan aikin da mu ke a fannin tsaro kamar haka ne aka yaba mana a wajen Jihar Kano”.

Sannan kuma, gwamna Ganduje ya tunasar da su cewa “da dama daga cikin manyan masu garkuwa da mutane an kame su a Jihar Kano. Mu na yi wa Allah godiya mun samu nasarar kawar da manyan ƙalubalen tsaro a Jiharmu”.

“Wannan nasara da mu ka samu a wannan wuri, Allah ne ya ba mu biyo bayan sanadin haɗin kai da gudunmawar da kowa ya bayar daga ɓangaren al’umma da kuma sassan hukumomin tsaro”.

Domin ƙara janyo hankalinsu kan cigaba da ba da ƙarin haɗin kai da goyon baya, gwamna Ganduje ya bayyana cewa tsaro ya na da matuƙar muhimmanci ga kowacce al’umma. Inda ya yi ƙarin haske cewa “babu wani cigaba da zai samu matuƙar babu ingantaccen tsarin tsaro mai tasiri”.

“Babu wani ƙoƙari da zai yi yawa, dan haka, tsaro shi ne muhimmin abun da mu ka sanya a gaba. Da taimakon Allah mu na da manyan abubuwa biyu da za su taimaka mana wajen cigaba da kare wannan matakin farin ciki da mu ke ciki kan amincin Jiharmu a bar alfaharinmu”.

Ƴan sandan cikin al’umma da aka ɗabbaƙa, na daga cikin manyan tsare-tsaren da su ka taimakawa Jihar. Inda ya bayyana yadda aka samar da kykkyawar alaƙa a tsakaninsu da kuma dukkan sassan hukumomin tsaro.

Kamar yadda ya ke cewa. “jami’an tsaronmu su na aiki hannu da hannu domin cigaba da samar da tsaro a Jihar Kano. Kuma babu wata rashin jituwa a tsakaninsu. Domin sun yi imanin su na da rawar takawa gaba ɗaya wajen ɗorewar zaman lafiya a muhallinmu.

Daga nan kuma sai gwamna Ganduje ya cigaba da cewa “nan ba da jimawa ba, za mu shirya taro na musamman dangane da batun ƴan sandan cikin al’umma. Ina ba ku tabbacin za ku kasance cikin taron. Kuma za ku kasance cikin al’umma masu amfani a gare mu. Na fahimci cewa ku na da maida hankali na musamman kan tsaro a wannan ƙasa tamu, ba shakka wannan abin yabawa ne.

Da ya ke gabatar musu da bayani kan wasu kayan aikin tsaro na musamman da Jiha ke amfani da su, gwamna Ganduje ya bayyana cewa Jihar Kano ta samar da motoci na zamani da kuma wasu kayan aikin na fiye da (Naira Miliyan 500) waɗanda kuma su ka game gaba ɗaya shiyar Arewa maso Yammacin Nageriya.

“Wannan motoci su na aiki gwanin yabawa. Nan ba da jimawa ba, za mu sanya na’urorin naɗar bayanai (CCTV) a duk faɗin Jihar Kano domin cigaba da inganta sha’anin tsaro a Jihar. Kuma akwai sauran tsare-tsare da dama da mu ke da su za mu aiwatar kan cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu”. Inji gwamna Ganduje.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Majalissar Zartarwa Ta Amince  A Kafa Ƙarin Masarautu Guda Huɗu U A Jihar Kano 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Kuma Tuni Ta Tura Ƙudirin Dokar Zuwa Gaban Zauren Majalissar Dokoki Na Jihar Kano.

Yau Litinin, 2 ga watan Disamba, 2019.
A wani zama da ta gudanar a daren Jiya Lahadi, majalissar zartarwa ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da ƙudirin dokar kafa ƙarin masarautu guda huɗu a Jihar Kano. Waɗanda su ka haɗa da masarautar: Bichi da Gaya da Rano da kuma Ƙaraye. Inda tuni kuma majalissar ta tura ƙudirin dokar zuwa gaban zauren majalissar dokoki na Jiha.

Sanarwar da aka fitar daga gidan gwamnati, ta kuma ƙara yin bayani da cewa dama can akwai wasu daga cikin waɗannan masarautu tun shekarun baya masu tsawo da su ka wuce, juyin zamani ne ya nemi ya shafe tarihinsu, kuma ko a zamanin janhoriya ta biyu sai da aka nemi a farfaɗo da su, amma aka samu tsaiko.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa majalissar zartarwa ta tattauna sosai game da alfanun ƙarin nasarautun kafin ta cimma wannan matsaya da ta ɗauka, ta kuma fahimci cewa ƙarin masarautun zai taimaka sosai wajen ƙara kusanci a tsakanin al’umma da sarakunan gargajiya. Sannan kuma ƙarin masarautun zai taimaka matuƙa wajen ƙara haɓaka harkokin kasuwanci da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Kano cikin hanzari.

Haka zalika, ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na ilimi kyauta kuma wajibi tun daga firamare har zuwa babbar sakandire, ya na buƙatar taka rawar al’umma sosai da sosai musamman ma sarakunan gargajiya domin samun nasarar shirin. Dan haka ƙarin masarautun zai taimaka sosai da sosai wajen cimma wannan buri.

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa ƙudirin dokar da aka ɗabbaka a zauren majalissaar dokoki a 2019, kotu ta rushe shi ne saboda mutum ne daga cikin al’umma ya gabatar da shi ba ɗaya daga cikin ƴan majalissa ba.

Kamar yadda sanarwar ta ƙara, majalissar zartarwar ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta kuma buƙaci zauren majalissar dokokin na Jihar Kano da su yi duba da buƙatun al’umma wajen amincewa da ƙudirin dokar.

Continue Reading

Labarai

Gwamna Ganduje Ya Taya Mallam Ibrahim Shekarau Murnar Samun Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-“Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa Da Aka Ba Wa Sanata Shekarau Alama Ce Da Ke Ƙara Shaida Yadda Duniyar Ilimi Ta Gamsu Da Irin Ɗumbin Gudunmawar Da Ya Ba Ta A Zamanin Da Ya Riƙe Matsayin Gwamna Da Muƙamin Ministan Ilimi Na Nageriya”. Inji Gwamna Ganduje.

Yau Asabar, 30 ga watan Nobemba, 2019.
Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano hawa biyu, kana kuma sanata mai ci, Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano murnar samun lambar yabo ta digirin girmamawa wanda Jami’ar Ritman da ke birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom ta ba shi a wannan rana ta Asabar.

Digirin girmamawar wacce jami’ar ta ba shi saboda irin ɗumbin gudunmawar da ya bayar a fannin iilimi a zamanin ya na matsayin gwamna da matsayin ministan ilimi, gwamna Ganduje ya taya shi murna a madadin gwamnatin Jihar Kano da al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya.

Kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar taya murnar da gwamna Ganduje ya bayar, “mai girma gwamna ya ga lambar yabo ta digirin girmamawa da aka ba wa Sanata Ibrahim Shekaru, inda lambar ke ƙara shaida yadda fannin ilimi ya gamsu da irin ɗumbin nasarori da gudunmawar da ya bayar a fannin da kuma gina rayuwar ɗan adam a lokacin da ya riƙe matsayin gwamna da kuma Ministan Ilimi a Nageriya.

Idan za a iya tunawa, ko a shekarar 2009, Sanata Shekarau ya samu irin wannan lambar yabo ta digirin girmamawa daga Jami’ar ƙasa ta Nsuka”. Sanarwar ta bayyana.

Inda kuma gwamna Ganduje ya ƙara da cewa wannan lambar yabo ga sanata Shekarau tambar ƙara zaburar da shi ne ya ƙara himma da ƙoƙari kan ƙoƙarin da ya ke na ba da gudunmawa wajen gina ƙasa da kuma gina rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Ya yin da ya ke taya Sanata Shekarau murnar wannan ƙarin matsayi da ya samu, gwamna Ganduje ya yi masa fatan alkhairi tare da fatan ya ƙara cigaba da dagewa wajen ba da gudunmawa kan cigaban ƙasa da sauran jama’a.

Continue Reading

Labarai

JAMI’AN TSARO SUN SAMU NASARAR KAME WANDA YA SHIRYA AURAR DA FATIMA GANDUJE TA BOGI

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ya Samar Da Fatima Ganduje Ta Bogi Ya Karɓi Kuɗi Kimanin Naira Miliyan Biyar Da Sunan Zai Ba Da Auren Fatima Ganduje Ta Gaske.

-Iyalan Gwamna Ganduje Sun Ba Da Umarni Jami’an Tsaro Su Cafke Duk Wani Ko Wata Da Za Su Bayyana Kansu A Matsayin Yaran Gidan Su Damfari Al’umma.

Yau Asabar, 23 ga watan Nobemba, 2019.
Jami’an tsaro sun samu nasarar kame wani matashi mai suna Abdullahi Zakari, wanda ya bayyana kansa a matsayin yaron gidan mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya damfari wani mutum mai sana’ar saida magunguna mai suna Alhaji Bashir Amadu Usaini da ke unguwar Tudun Yola zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan Biyar da sunan wai zai haɗa shi da ƴar mai girma gwamna Fatima Ganduje ya aura.

Yadda lamarin ya faru shi ne: tun kafin Fatima Ganduje ta yi aure, Abdullahi Zakari ya samu wani mai suna Alhaji Bashir Amadu ya kwaɗaita masa cewar shi yaron gidan gwamna Ganduje ne, dan haka ya yi masa alƙawarin zai haɗa shi aure da Fatima Ganduje. Sannu a hankali har ta kai ga wannan ɗan damfara (Abdullahi Zakari) ya samar da Fatima Ganduje ta ƙarya ya haɗa su da Alhaji Bashir Amadu su na waya da juna da sunan soyayya.

Sannu-sannu har ta kai ga wannan Fatima ta bogi ta na neman kuɗi a wurin Alhaji Bashir Amadu inda ta ke shaida masa cewar wai auren dole za a yi mata a gida, dan haka ba ta tambayar kowa kuɗi in ba shi ba, saboda shi ta ke so ta aura.

Sannan kuma, shi wannan ɗan damfara ya samar da wata matar ta bogi a matsayin Balaraba Ganduje, wato yayar Fatima Ganduje, ta yadda duk kuɗin da Fatima Ganduje ta bogi za ta nema a wurin Alhaji Bashir Amadu, ita wannan Balaraba Ganduje ta bogin ce ta ke ƙara ba shi tabbacin da ƙarfin gwiwa kan ya ba da ko nawa ne ta tambaye shi saboda wai ita Fatiman ba ta tambayar kowa kuɗi a gidan nasu sai shi saboda shi ne ta ke son zai aure ta, wanda hakan ne kuma ya ke sanya shi ko da yaƙi ko kuma ba shi da kuɗi a lokacin to wannan ƙaimi da Balaraba Ganduje ta bogin ta ke yi masa kan sa shi ya nemo ya bayar.

Bayan haka, shi dai wannan ɗan damfara, har Gwaggo wato Hajiya Gafsat Ganduje ya samar ta bogi, inda ya sanya ita waccar Fatiman bogin ta nemi wayar mahaifiyar shi wanda ake damfara ɗin, Bashir Amadu ta haɗa su da wannan Gwaggo ta bogi su ka gaisa da mahaifiyarsa a lokacin da ba ta da lafiya.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da Fatima Ganduje da Balaraba Ganduje da kuma (Gwaggo) Hafsat Ganduje duk na bogi kafin Fatima Ganduje ta gaske ta yi aure har tsawon kusan shekaru uku.

Sannan bayan Fatima Ganduje ta gasken ta yi aure, duk da haka ba su ƙyale shi ba, wannan Fatima Ganduje ta bogin ta cigaba da yi masa waya ta na faɗa masa cewar ita fa ba zaman auren nan za ta yi ba domin dole aka yi mata dan haka za ta kashe auren ta fito ta aure shi.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da waɗannan mata a matsayin ƴaƴa ne na gwamna, wato Fatima da Balaraba, da kuma mahaifiyarsu Gwaggo ya yi ta karɓan kuɗi a hannun wannan bawan Allah mai suna Bashir Amadu Usaini har kimanin Naira Miliyan Biyar cikin shekaru uku da su ka shafe.

Sai dai jami’in tsaro sun samu nasarar kame wannan ɗan damfara, har ma an gurfanar da shi a gaban kotun Noman Salak da ke nan Jihar Kano a jiya, kuma alƙali ya tura shi zaman gidan kaso kafin a nemo sauran matan da ya yi amfani da su wajen shirya wannan damfara da zamba a dawo a cigaba da shari’ar.

Sannan kuma tuni iyalan mai girma gwamna sun ba da gargaɗi kan a guji yarda da duk wani wanda zai je wa da wani da irin wannan alaƙa, sannan kuma duk wanda aka kama to ayi gaggawar sanar da jami’an tsaro mafi kusa domin su kame shi.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending