Connect with us

Rahotonni

Rahoto: Kano na cikin jihohi 4 da zasu iya aiwata da kasafin kudi cikin nasara a 2020

Published

on

RAHOTON BINCIKE: JIHOHI HUƊU NE KACAL A NAGERIYA ZA SU IYA AIWATAR DA KASAFIN KUDIN SHEKARAR (2020) CIKIN NASARA CIKI KUWA HAR DA JIHAR KANO TA GWAMNA GANDUJE

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Yau Lahadi , 27 ga watan Octoba, 2019.
A wani sakamakon bincike da aka fitar a ranar Laraba, 23 ga watan Octoba, 2019, daga wata ƙungiya mai zaman kanta wacce ke bibiyar al’amuran kasafin kuɗin shekara-shekara a Nageriya, ta bayyana cewa a duk Nageriya Jihohi guda huɗu ne kacal za su iya aiwatar da kasafin kuɗin shekarar (2020) cikin nasara.

Rahoton binciken wanda aka yi masa take da “Jiha zuwa Jihohi, ya bayyana Jihohin Jihar Legas a matsayin ta farko, sai kuma Jihar Rivers a matsayin ta biyu, ya yin da Jihar Akwa Ibom ta ke a matsayin Jiha ta uku sai kuma Jihar Kano a matsayin Jiha ta huɗu.

Rahoton binciken wanda aka gabatar da shi ga mai girma gwamnan Jihar Kaduna ta hannun shugaban ma’aikatansa, Mallam Muhammad Sani. Da kuma gwamnan Jihar Ekiti, ta hannun mataimakinsa na musamman kan al’amuran masana’antu Akintunde Oyebode.

Rahoton wanda aka gabatar da shi daga ƙarƙashin jami’in bincike da nazari da kuma tsare-tsare kan kasafin kuɗi, Mista Ojiugo Uche ya bayyana rauni kan tattalin arziƙin Jihohi musamman ma ta fuskar rashin tsarin gasa cikin masana’antu da kuma harkokin kasuwanci. Tare da tsame Jihohin Legas da Rivers da Delta da Ogun da kuma Akwa Ibom da Kano.

A cikin rahoton an bayyana cewa “A haƙiƙanin gaskiya mafi yawan Jihohin Nageriya ba su tsarawa kansu hanyoyin da za su bi su kafu su kuma iya tsayawa da ƙafafunsu kan samar da tattalin arziƙi na ƙashin kai ba. Hanyoyin da su ke bi a yanzu ba sa gamsarwa. Sannan akasari sun fi karkata kan kason kuɗin da su ke samu wata wata daga gwmnatin tarayya.

“A rahoton bincike na shekarar (2019), mun sauya hanyoyin da mu ke bi wajen gudanar da bincike, inda mu ka koma mu ke amfani da haƙiƙanin abubuwan da aka tsara kashewa a Jiha, mu ka kauda batun zaton abubuwan da ba su da tabbas kan manyan abubuwa”.

“Kasafin kuɗin da gwamnatocin Jihohi su ke amfani da su wajen nazarin bayanan kuɗaɗen shiga a duk Jihohi (36) na Nageriya. Mun yi aikin tabbatar da ganin cewa kasafin kuɗin ya tafi kan tsare-tsare na zahiri a dukkan gwamnatioci”.

“A wannan rahoto, Jihar Legas ta na jan ragamar bayyanannen tsarin tattalin arziƙi mai ɗorewa. Mai bi mata kuma ita ce Jihar Rivers da Akwa Ibom da Jihar Kano”.

“Kuma a haƙiƙanin gaskiya su ne Jihohin da nazari da bincike ya tabbatar da za su iya tunƙarar duk wani ƙalubalen harkokin kuɗi kai tsaye”. Rahoton binciken ya yi bayani.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Rahotonni

Gwamna Ganduje ya fara raba kayan makaranta kyauta ga dalibai

Published

on

By

JIHAR KANO A MAKO MAI ƘAREWA (15)

TSARAWA DA GABATARWA Bashir Abdullahi El-bash

-A Wannan Mako Mai Ƙarewa, Gwamna Ganduje Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayan Makaranta Kyauta Ga Ɗalibai Da Kuma Raba Kayayyakin Koyo Da Koyarwa Ga Makarantun Firamare A Jihar Kano.

Yau Juma’a 25 ga watan Octoba, 2019.
Kamar yadda aka saba, a wannan mako ma ga ni tafe da wani sabon shirin wanda a bisa al’ada Ni Bashir Abdullahi El-bash na saba kawo muku muhimman batutuwa masu alaƙa da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatinsa waɗanda su ka faru a makon da mu ke daf! Da yin bankwana da shi.

(1). A wani mataki na nuna gamsuwa kan nasarorin da aka cimma a fannin lafiya a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a wannan mako mai ƙarewa ne, asusun duniya mai fafutukar yaƙi da: tarin (TB, HIV, da kuma zazzaɓin cizon sauro, Malaria), ya ba da tabbacin zai kashe fiye da (Naira Biliyan 11) a Jihar Kano domin kauda zazzaɓin na maleriya gaba ɗaya daga (2018-2020).

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin bayanan da jami’in asusun a Nageriya, Dakta Ibrahim Faria ya yi a ya yin wata ziyara da su ka kai wa mai girma gwamnan a ofishinsa da ke gidan gwamnatin Jihar Kano.

A cikin jawabin da ya gabatar, Dakta Faria ya ƙara da yin yabo cewa, “mu na matuƙar farin ciki kan yadda Jihar Kano ta zama jagabar sauran Jihohi wajen kula da tsarin kiwon lafiya. Haƙiƙa lamarin ya zo da bazata kuma abin ƙarfafa gwiwa. Mai girma gwamna, ina mai tabbatar maka cewa a kowane lokaci za ka zama abin misali a garemu”. Inji Dakta Faria.

A ya yin da ya ke maida jawabi, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ba su tabbacin cigaba da samun haɗin kan gwamnatinsa. Sannan ya kuma ƙara da cewa: “Akwai buƙatar mu yi abubuwa da dama a fannin yaƙi da tarin TB, domin wasu daga cikin al’umma su na ganin kamar tarin tibi wata alama ce ta kamuwa da cuta mai karya Garkuwar jiki (HIV). Su na buƙatar a samar da gangamin wayar da kai sosai akan wannan”. Cewar Gwamna Ganduje.

(2). A ƙoƙarin kai Jihar Kano kan matakin ƙololuwar cigaba a fannin lafiya, da sauran fannoni, kamar yadda ya samar da ƙarin sabbin masarautu, a wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kira ƴan kwangila da su nemi aikin gina sabbin asibitoci irin na zamani da gwamnatinsa za ta bayar a yi a manyan biranen sabbin masarautu guda (4) da ya kirkiro waɗanda za su ɗauki gadajen kwantar da marasa lafiya a ƙalla guda ɗari huɗu (400).

Kamar yadda mai girma gwamna ya bayyana gwamnati za ta yi amfani da wannan sabbin masarautu da ta ƙirƙiro domin ƙara inganta sha’anin kiwon lafiya a wannan gwamnati. Wannan yunƙuri ma a cewar gwamna Ganduje wani mataki ne na tunkarar ƙudurorin da ake da su.

Kamar yadda ya ke cewa: “Jihar Kano za ta ƙara ƙaimi wajen ƙara haɓaka sha’anin kiwon lafiya a dukkan sabbin masarautunmu huɗu. Wannan ƙuduri, ɗaya ne daga cikin ɗumbin abubuwan da za mu cimma wajen ɗaga darajar abubuwan kula da lafiya a manyan biranen masarautun. Tayadda kuma kowanne asibiti ɗaya za ya ɗauki gadaje a ƙalla guda (400) na kwantar da marasa lafiya”. Cewar Gwamna Ganduje.

(3). A wannan mako mai ƙarewa, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi baƙuncin wakilan shugabannin ƙananan hukumomi ƙarƙashin ƙungiyarsu ta (ALGON) reshen Jihar Kano bisa jagorancin mataimakin shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne shugaban ƙaramar hukumar Bunkure Onarabul Rabi’u Bala inda su ka ziyarce shi a masauƙinsa na gwamna da ke Asokoro babban birnin tarayya Abuja domin taya shi murnar nasara da ya samu a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe.

A cikin jawabin da ya gabatar, mai girma gwamna ya ba su tabbacin gwamnatinsa na cigaba da yin aiki tare da su kafaɗa da kafaɗa domin cigaba da samar da cigaba a ƙananan hukumominsu da ma Jiha gaba ɗaya, inda ya ƙara musu ƙwarin gwiwa da cewa: “ku kasance masu kusanci da kykkyawar dangantaka da al’umma a ƙananan hukumominku, a kowane lokaci ku zamto masu himma da ƙoƙarin fahimtar al’ummominku domin cigaba da kyautata rayuwarsu”. Inji gwamna Ganduje.

Tunda farko a nasa jawabin, mataimakin shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin, (ALGON) ta Jihar Kano, Onarabul Bala, ya taya mai girma gwamna murna tare da ba shi tabbacinsu na cigaba da marawa gwamnatinsa baya wajen ciyar da Jihar gaba.

Daga ƙarshe kuma, dukkanninsu sun godewa mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje dangane da irin goyon baya da haɗin kan da ya ke ba su wajen tafiyar da ƙananan hukumominsu cikin nasara da aminci.

(4). A wannan mako mai ƙarewa ne, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya aikewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Kwankwason saƙon taya shi murnar zagayowar ranar da aka haife shi. Kamar yadda ya ke cewa:

“A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya, mu na taya mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa inda ya cika shekaru (63) yau a Duniya. Mu na yi masa fatan samun ƙarin shekaru cikin ƙoshin lafiya da nasara a rayuwa ta gaba”.

(5). A wani mataki na yabawa da ɗumbin cigaban da ya samar wajen inganta sha’anin noma da kyautata fannin kiwon lafiya, a wannan mako mai ƙarewa, gidan Jaridar (Business Day), ta zaɓi mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan da ya fi kowane gwamna ƙoƙarin haɓaka harkokin noma da kyautata sha’anin kiwon lafiya a Nageriya cikin shekarar (2019) biyo bayan binciken ƙwaƙwaf da nazari mai zurfi da su ka yi a Jihohi (36) gaba ɗaya.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wasiƙar da aka aikewa mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a ranar 7 ga watan Octoba, 2019, mai ɗauke da sa hannun mawallafin jaridar, kana kuma shugaban kamfanin jaridar gaba ɗaya, Mista Frank Aigbogun.

Takardar ta fara da bayyana cewa: “Mai girma gwamna, kwamitin shirya gasar Lashe Lambar yabo ta Jihohi kan shugabanci da jagoranci na ƙwarai a shekarar (2019), na farin cikin sanar da kai ka samu nasarar zama gwamnan da ya fi kowane gwamna inganta sha’anin noma da kyautata harkokin kula da kiwon lafiya a Nageriya”.

“Mai girma gwamna, kwamitin tsara wannan lambar yabo, na farin cikin yin amfani da wannan dama wajen taya ka murnar wannan nasara da ka samu”.

(6). A wannan mako mai ƙarewa, rundunar jami’an tsaro ta ƴan sanda ta ƙasa a Jihar Kano, ta miƙawa gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje yara guda bakwai daga cikin taran da aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane waɗanda aka sace su aka kai su Jihar Anambara aka sayar da su aka kuma sauya musu addini.

A ya yin da ya ke karɓar yaran a ɗakin taro mai suna (Africa House) da ke cikin gidan gwamnati, a madadin mai girma gwamna, sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya bayyana gano yaran a matsayin wani gagarumin aiki abin sambarka, inda jami’an tsaro na ƴan sanda su ke ƙoƙari matuƙa wajen yaƙi da ayyukan laifi.

A ya yin miƙa yaran ga mai girma sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, a madadin mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kwamandan rundunar ƴan sanda ta musamman kan yaƙi da masu garkuwa da mutane na Jihar Kano, (CSP) Babagana Saje, ya yi bayani cewa, “iyaye bakwai sun gane ƴaƴansu bayan ɗaukwar matakin bin tsari irin na tsaro.

Amma har yanzu akwai biyu da su ke iƙirari. Dan haka mu na umartar iyayen da aka sace musu yara a Kano da su daure su zo ofishinmu domin tantance sauran yara biyun da su ke hannunmu”.

Daga nan kuma sai ya ba da tabbacin gurfanar da duk waɗanda ake zargi da satar yaran a gaban kotu nan gaba kaɗan da zarar sun kammala binciken da su ke.

Da ya ke gabatar da jawabi a madadin iyayen yaran Mallam Muhammad Ali, ya yi bayani cewa tun shekarar (2016) aka sace masa tasa ɗiyar (A’isha). Kuma dukkan iyaye sun yi farin ciki da aka gano musu ƴaƴansu. Daga nan kuma sai ya yabawa jami’an tsaron rundunar ƴan sanda tare da gode musu dangane da wannan gagarumin aiki da su ka ka yi.

(7). A ƙoƙarinsa na cigaba da haɓaka tattalin arziƙin Jiha da kuma cigaba da kyautata dangantakar tattalin arziƙi da sauran ƙasashen Duniya, a wannan mako ne aka tsara mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai kai wata ziyarar aiki zuwa ƙasar Faransa inda zai gana da manyan ƴan kasuwa na ƙasar domin jawo hankulan masu zuba jari wajen ƙara ƙarfafa dangantakar tattalin arziƙi da ta al’adu a tsakanin Jihar Kano da kuma ƙasar ta Faransa.

Daga cikin ginshiƙan ziyarar tasa, har da batun ganawa ta musamman tare da ɗalibai ƴan asalin Jihar Kano waɗanda su ke karatu a ƙasar ta Faransa a cikin jami’o’i daban-daban na ƙasar inda wasu su ke matakin digiri na biyu wasu kuma su na kan matakin digirin-digirgir.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a ya yin da ya ziyarci ofishin jakadancin Faransa da ke Abuja inda ya gana da jakadan ƙasar Mista Jeremo Pasquier a wannan rana ta Talata, inda kuma ya ba shi tabbacin yin iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya samo gagarumar nasara kan tattalin arziƙin Jihar Kano wajen ganawa da manyan ƴan kasuwa na ƙasar ta Faransa dazarar ya je.

A ya yin da ya ke maida jawabi, jakadan ƙasar ta Faransa a Nageriya, Mista, Pasquer, ya yabawa gwamna Ganduje kan yadda ya ke gudanar da kykkyawan aiki tuƙuru a fannin ilimi da kuma sauran fannoni a gwamnatinsa.

Daga nan kuma sai ya ƙara da ba da tabbacin ƙasarsu ta Faransa wajen cigaba da marawa gwamnatin Jihar Kano baya kan fannin ilimi da kuma tabbatar da kykkyawar alaƙar dangantakar tattalin arziƙi a tsakanin ƙasar da kuma Jihar Kano.

(8). A wannan mako mai ƙarewa, a wani yanayi da ke nuni da yadda ta ke koyi da mahaifinta kan riƙo da addini, a ƙarƙashin jagorancin, Hajiya Balaraba, Abdullahi Umar Ganduje yara ƙanana ƴan ƙasa da shekaru (20), sun yi saukwar Al-qur’ani mai girma domin nuna godiya ga Allah mai girma da ɗaukaka kan nasarar da ya ba wa mai grma Gwamnan Jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a zagayen mulki na biyu.

(9). A wannan mako mai ƙarewa, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙaddamar da rabon kayan sawa na makaranta (Uniforms) ga ɗalibai da kuma kayayyakin koyo da koyarwa ga makarantun Firamare a wani mataki na fara aiki da shirin ilimi kyauta kuma wajibi da ya ƙaddamar kwanakin baya a Jihar Kano tun daga Firamare har zuwa babbar Sakandire.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a makarantar Firamare ta Mariri mai suna (Mariri Special Primary School) da ke ƙaramar hukumar Kumbotso.

Kimanin kayan sawa na makaranta (Uniforms) guda (29,480) mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya raba ga ɗalibai ƴan aji ɗaya na dukkan makarantun Firamare guda (78) da ke faɗin ƙaramar hukumar ta Kumbotso a wannan rana.

A fannin kayan aiki na koyo da koyarwa kuwa, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya raba Littattafai na aiki guda (500) da kuma Littattafan karatu na Hausa guda (500) da kuma (Flash Card) guda (50).

A ya yin da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron ƙaddamar da rabon kayan, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa: “tuni gwamnatin Jihar Kano ta fara tura kuɗaɗe cikin asusun ajiyar Banki na makarantun Firamare da na Sakandire guda (1,180) masu jimillar ɗalibai guda (834, 366) inda za su riƙa samun kimanin (Naira Miliyan 200) a duk ƙarshen wata, inda ya kama (Naira Miliyan 2.4) a duk shekara”.

Sannan kuma, gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta sake samar da sabbin kayan sawa na makaranta (Uniforms) ga sabbin ɗalibai maza da mata kimanin guda (779,522) a kan kuɗi kimanin (Naira Miliyan 381).

Kuma kamar yadda aka ƙaddamar da wannan, haka mai girma gwamna zai cigaba da zagayawa sannu a hankali har sai ya gama da dukkan ƙananan hukumomin Jihar Kano guda (44) gaba ɗaya.

(10). A wannan mako mai ƙarewa, mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci bikin kammala Musabaƙar karatun Al-Qur’ani mai girma karo na goma sha ɗaya, (11) wanda aka gudanar a ƙarƙashin (Gidauniyar Ganduje) a dukkan masarautu guda biyar (5) na Jihar Kano gaba ɗaya domin samun nasarar zaɓen Jihar.

(11). A wannan mako mai ƙarewa, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tare da shugaban jam’iyyar (APC) na ƙasa, Kwamared Adams Oshimole, haɗe kuma da manyan jiga-jigan jam’iyyar na ƙasa, sun halarci gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan Jihar Bayelsa na jam’iyyar ta (APC). Kuma gwamna Ganduje ya na cikin babban kwamitin yaƙin neman zaɓen da uwar jam’iyya ta ƙasa ta kafa.

(12). A wannan mako mai ƙarewa, haɗakar fulani makiyaya daga Nahiyar Turai da ƙasar Amurka waɗanda tushiyarsu ta ke a Nahiyar Afrika, sun zaɓi mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin babban uba ga ƙungiyar, tayadda kuma ya zamto ɗan Afrika na farko da ya ya taɓa samun wannan matsayi a ƙungiyar.

A wasiƙar da su ka aikewa mai girma gwamna mai ɗauke da sa hannun babban sakataren ƙungiyar, Muhammad Farouƙ Auwalu, kan shaida masa wannan zaɓa tasa da su ka yi, sun yi bayani cewa:

“mai girma gwamna, ƙoƙarin da ka ke a gwamnatinka, domin kyautata rayuwar fulani makiyaya a Nageriya, ba shakka ka cancanci yabo daga wannan ƙungiya tamu, saboda waɗannan dalilai, mu ka ga dacewar mu nemi ka zama babban uba ga wannan ƙungiya”.

“Ƙungiyarmu ta Fulani makiyaya ta Nahiyar Afrika kan zaman lafiya da samar da cigaba, mu na zaɓar mutum ne mai nagarta da daraja wanda ya ke shimfiɗa shugabnci nagari ga fulani makiyaya a Nahiyar Afrika kowane lokaci. Wanda kuma ya ke ƙoƙari da fafutuka a kansu”.

“Mai girma gwamna, kasancewar ka babban uba ga wannan ƙungiya, zai taimaka mana matuƙa wajen samun nasarar cimma manufofi da muradan wannan ƙungiya kan fafutukar kare haƙƙin fulani makiyaya a Nahiyar Afrika.

(13). A wani mataki na ƙoƙarin bin haƙƙoƙin yara (9) da aka ceto bayan an yi garkuwa da su an kai su Jihar Anambara, a wannan mako mai ƙarewa, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi domin gudanar da binciken ƙwaƙwaf a ƙarƙashin jagorancin tsohon mai shari’a Wada Umar Rano, kuma mai girma gwamna zai ƙaddamar da kwamitin a ƙarshen wannan wata ranar Alhamis, 31 ga watan Octoba, 2019. In Insha Allahu.

(14). A wannan mako mai ƙarewa, mai girma gwamnan Jihar kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karɓi baƙuncin Ministan Noma na Nageriya, Mallam Sabo Nanono inda inda za su gudanar da taro na musamman kan harkokin noma da manoma a Jihar Kano.

Continue Reading

Labarai

Kungiyar lauyoyi ta kaiwa gwamna Ganduje ziyara

Published

on

By

ƘUNGIYAR LAUYOYIN NAGERIYA TA GUDANAR DA TATTAKIN JADDADA GOYON BAYA GA GWAMNA GANDUJE

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ƙungiyar Ta Kuma Yabawa Gwamna Ganduje Kan Ƙoƙarinsa Na Haɓaka Tsaro A Jihar Kano

-Gwamna Ganduje Ya Ba Da Tabbacin Maƙala Na’urar Naɗar Bayanai (CCTV) A Loko Da Saƙo Na Jihar Kano Domin Cigaba Da Inganta Tsaro A Jihar Gaba Ɗaya.

-Sannan Kuma, Gwamna Ganduje Zai Shirya Taro Na Musamman Kan Ƴan Sanda Na Cikin Al’umma

Yau Asabar, 26 ga watan Octoba, 2019.
Ƙwararrun Lauyoyi a Jihar Kano ƙarƙashin ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA), a wannan rana sun ziyarci gidan gwamnatin Jihar Kano domin nuna goyon bayansu da kuma girmamawa ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan yadda ya tunkari ƙalubalen matsalar tsaron Jihar da ya kunno kai a wannan yanayi baya-bayan nan.

Mai girma gwamna ya karɓe su ne a babbar ƙofar shiga gidan gwamnati da ke babban titin Jihar, a ya yin da shugaban ƙungiyar ta Lauyoyin Nageriya (NBA) reshen Jihar Kano, Barista, Musa Abdul Lawan ya gabatar da jawabin ba da tabbacin goyon bayansu da kuma girmamawarsu ga gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamna Ganduje. Inda ya kuma ƙara da cewa: “ba wai reshen Kano ne kaɗai na ƙungiyar ta (NBA) ba, har da reshen ƙaramar hukumar Ungogo su ma mun samu goyon bayansu kan wannan ziyarar girmamawa da nuna goyon baya”.

Kamar yadda shugaban ƙungiyar ya bayyana ƙungiyar ta shirya taro a Jihar dangane da batun ƙalubalen matsalar tsaro da ya kunno kai, “mai girma gwamna dukkan ƙoƙarinka na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano ya gamsar. Mu na ba ka tabbacin kasancewa a bayanka a kowane lokaci domin tabbatar da cewa Jihar Kano ta cigaba da kasancewa cikin aminci”.

Inda ya ƙara bayyana farin cikinsa da cewa “ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kano wajen tabbatar da aminci a Jihar a kowane lokaci za mu cigaba da mara mata baya. Mu na alfaharin cewa Jihar Kano ta na cikin aminci. Allah ya ƙaro alkhairi da cigaba mai girma gwamna”.

A ya yin da ya ke maida jawabi, gwamna Ganduje ya ba su tabbacin gwamnatinsa na cigaba da mutunta doka da oda a kowane lokaci. Tare kuma da ƙara ƙarfafa fannin shari’a da kuma wanzar da kykkyawan jagoranci kan fannin shari’ar Jihar.

Daga nan kuma sai ya ƙara da yin godiya ga wannan ƙungiya ta ƙwararrun lauyoyi kan wannan goyon baya da ƙara ƙarfafa gwiwa da su ka bayyana masa, kamar yadda ya ke cewa “wannan yabo naku gare mu kan kykkyawan aikin da mu ke a fannin tsaro kamar haka ne aka yaba mana a wajen Jihar Kano”.

Sannan kuma, gwamna Ganduje ya tunasar da su cewa “da dama daga cikin manyan masu garkuwa da mutane an kame su a Jihar Kano. Mu na yi wa Allah godiya mun samu nasarar kawar da manyan ƙalubalen tsaro a Jiharmu”.

“Wannan nasara da mu ka samu a wannan wuri, Allah ne ya ba mu biyo bayan sanadin haɗin kai da gudunmawar da kowa ya bayar daga ɓangaren al’umma da kuma sassan hukumomin tsaro”.

Domin ƙara janyo hankalinsu kan cigaba da ba da ƙarin haɗin kai da goyon baya, gwamna Ganduje ya bayyana cewa tsaro ya na da matuƙar muhimmanci ga kowacce al’umma. Inda ya yi ƙarin haske cewa “babu wani cigaba da zai samu matuƙar babu ingantaccen tsarin tsaro mai tasiri”.

“Babu wani ƙoƙari da zai yi yawa, dan haka, tsaro shi ne muhimmin abun da mu ka sanya a gaba. Da taimakon Allah mu na da manyan abubuwa biyu da za su taimaka mana wajen cigaba da kare wannan matakin farin ciki da mu ke ciki kan amincin Jiharmu a bar alfaharinmu”.

Ƴan sandan cikin al’umma da aka ɗabbaƙa, na daga cikin manyan tsare-tsaren da su ka taimakawa Jihar. Inda ya bayyana yadda aka samar da kykkyawar alaƙa a tsakaninsu da kuma dukkan sassan hukumomin tsaro.

Kamar yadda ya ke cewa. “jami’an tsaronmu su na aiki hannu da hannu domin cigaba da samar da tsaro a Jihar Kano. Kuma babu wata rashin jituwa a tsakaninsu. Domin sun yi imanin su na da rawar takawa gaba ɗaya wajen ɗorewar zaman lafiya a muhallinmu.

Daga nan kuma sai gwamna Ganduje ya cigaba da cewa “nan ba da jimawa ba, za mu shirya taro na musamman dangane da batun ƴan sandan cikin al’umma. Ina ba ku tabbacin za ku kasance cikin taron. Kuma za ku kasance cikin al’umma masu amfani a gare mu. Na fahimci cewa ku na da maida hankali na musamman kan tsaro a wannan ƙasa tamu, ba shakka wannan abin yabawa ne.

Da ya ke gabatar musu da bayani kan wasu kayan aikin tsaro na musamman da Jiha ke amfani da su, gwamna Ganduje ya bayyana cewa Jihar Kano ta samar da motoci na zamani da kuma wasu kayan aikin na fiye da (Naira Miliyan 500) waɗanda kuma su ka game gaba ɗaya shiyar Arewa maso Yammacin Nageriya.

“Wannan motoci su na aiki gwanin yabawa. Nan ba da jimawa ba, za mu sanya na’urorin naɗar bayanai (CCTV) a duk faɗin Jihar Kano domin cigaba da inganta sha’anin tsaro a Jihar. Kuma akwai sauran tsare-tsare da dama da mu ke da su za mu aiwatar kan cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu”. Inji gwamna Ganduje.

Continue Reading

Rahotonni

Nan bada jimawa ba zan bayyana sunayen kwamishinoni na -Ganduje

Published

on

By

GWAMNA GANDUJE YA BAYYANA CEWA “NAN BA DA JIMAWA BA ZAI BAYYANA SUNAYEN SABBIN KWAMISHINONINSA”

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Yau Lahadi, 27 ga watan Octoba, 2019.
Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da cewa nan gaba kaɗan ne zai sanar da sunayen membobin kwamitin majalissar zartarwa na Jiha (Kwamishinoninsa), inda ya kuma ƙara da ba da tabbacin gwamnatinsa wajen cigaba da gudanar da managartan ayyuka kamar yadda ya faro a wa’adin zangon mulkinsa na farko.

Sannan kuma gwamna Ganduje ya yabawa sakatarorin dindindin na sassan ma’aikatun da ke faɗin wannan Jiha. Tare kuma da ba da tabbacin gwamnatinsa na ƙaddamar da kwamishinoni a ma’aikatun. Amma sakatarorin dindindin a ma’aikatun su na da damar gabatar da takardun bayanai ƙarƙashin aikin haɗin gwiwa a yau kafin gabatarwar ƙarshe ga zauren majalissar dokoki ta Jiha.

“Nan kusa, za mu samar da kwamishinoni a wuraren. A saboda haka za mu cigaba bibiyar manufofi da tsare-tsare da ayyukanmu. Ayyukanku a matsayin ma’aikatan gwamnati kan waɗannan takardu, ƙarara ya bayyana cewa aikin gwamnati shi ne ginshiƙin duk wata gwamnati”.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a yau Lahadi, a ya yin wani zama da ya yi da dukkan sakatarorin dindindin ɗin na ma’aikatu a zauren majalissar zartarwa na Jiha da ke ofishin gwamnan inda su ka gabatar masa da ƙunshin takardu kan tsare-tsaren kasafin kuɗi, a wani mataki na ƙarshe kan kammala kasafin.

“Tuni mun kammala dukkan wasu tsare-tsare, abin da ya rage mana shi ne nazari da bibiyar takardun kasafin kafin gabatarwa ta ƙarshe a zauren majalissar dokoki na Jiha”.

“Babban abin duba kan kasafin kuɗin shi ne gina rayuwar al’umma. Wadda kuma shi ne babban matakin gina cigaban Jiha. Za mu maida hankali sosai a dukkan wasu fannoni da ɓangarori a wannan Jiha. Sannan za mu yi ƙoƙari matuƙa wajen kammala ɗumbin ayyukan da ba a kammala ba”.

Da ya ke tsokaci game da shirinsa na ilimi kyauta kuma wajibi tun daga Firamare har zuwa babbar Sakandire, gwamna Ganduje ya bayyana cewa idan ya ce “kyauta”, to “kyautar” ya ke nufi, sannan in ya ce “wajibi”, to “wajibin” ya ke nufi.

“Idan mu ka ce kyauta, to a lokaci guda mu na maida hankali kan muhallin koyarwa da kuma kayayyakin koyo da koyarwa da sauransu. Mu na yi wa Allah godiya kan yadda mu ka samu damar inganta shigar da yara makaranta tun bayan da mu ka ƙaddamar da fara aiwatar da shirinmu na ilimi kyauta kuma wajibi”.

Gwamna Ganduje ya kuma cigaba da bayani cewa: “idan mu ka yi maganar wajibi, a lokaci guda mu na magana ne kan tsare-tsare da hanyoyin bi wajen cimma wannan ƙuduri. Idan mu ka yi magana kan sha’anin kiwon lafiya, mu na magana ne kan kyautata tsarin kula da kiwon lafiya. Kan waɗannan nufi namu, Za mu cigaba da samar da kayayyaki da abubuwan kula da lafiya da sauransu da sauransu”.

A kan masarautu, gwamna Ganduje ya tunatar da cewa, za su samar da sauƙin samar da cigaba a gundumominnsu, “babu wani abu sama da wannan, kuma wannan shi ne nufinmu na kyautata rayuwa da fannonin cigaban al’umma. Ta hanyar waɗannan masarautu, za mu ratsa cigaba ya riski al’umma tun daga tushe. Muradinmu shi ne cigaba da kyautata shigar da jama’a cikin manyan muhimman fannoni na ilimi da na lafiya da tsaro da kuma fannin noma”.

Daga nan kuma gwamna Ganduje ya ba da tabbacin fitar da kasafin kuɗin cikin inganci, inda ya ƙara da haskaka yadda aka bi matakin tsara kasafin kuɗin kamar yadda ake yi a duniya tun daga matakin farko har zuwa wannan gaɓa da ake kai a yanzu ya yin taron. Kuma za ta cigaba da wanzuwa har zuwa matakin ƙarshe.

A nasa jawabin, shugaban ma’aikata na Jiha, Dakta Kabiru Shehu, bayan ya yabawa gwamna Ganduje kan ayyukan raya Jiha da ya aiwatar, ya kuma ba da tabbacin dukkan ma’aikatan Jiha wajen cigaba da haɗa hannunsu kan cigaba da gina jihar da kuma kyautata rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Sannan kuma a madadinsa da kuma dukkan sakatarorin dindindin na ma’aikatu, sun gabatar da kyaututtuka ga mai girma gwamna a matsyin wata alama da ke nuna farin cikinsu da kuma taya murnar samun nasara da mai girma gwamnan ya yi a kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamna. Tare da ba da tabbacin cewa “Kamar yadda mu ka ba da goyon bayanmu a gare ka kan wa’adin zangon mulki na biyu cikin fatan nasara, mu na da tabbacin cewa dukkan manufofi da tsare-tsarenka za su zamto gamsassu kan samar da cigaba mai ma’ana a kowane fanni”.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending