Connect with us

Siyasa

Sheikh Kabiru Gombe ya fadi gaskiya kan gwamna Ganduje

Published

on

KALAMAN SHEIKH KABIRU HARUNA GOMBE A KAN GWAMNA GANDUJE

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Yau Alhamis, 24 ga watan Octoba, 2019.
“Allah ya sani, da Allah zai tambayen mai ya sa ka ce musu su zaɓi Ganduje ? Wallahi akwai dalilan da na dogara da su, kuma ina sa ran Allah ya yarda da su”.

“Kwanaki ya gayyace mu musuluntar da Maguzawa, Bamaguje ɗari biyu da kiristoci biyu, sun musulunta a sanadiyyar shi. Bayan wannan na samu labarin an sake yi a wudil, Bamaguje ɗari biyu ya sake musulunta”.

“Ranarda mu ka je aka musuluntar da Bamaguje ɗari biyu, Allah ya sani kuka na rinka yi na ga abin da ban taɓa gani ba. In ga wahalar da mu ke sha in mun shiga ƙasashen arna kafin mu samu mutum goma, ashirin, talatin, yau ga mutum ɗari biyu da biyu a gabana za su karɓi kalmar Shahada”.

“Shugaban ƙungiya na ƙasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau, sai da ya ba da kalmar shahada wa mutum talatin. Ni da kaina sai da na ba da kalmar shahada wa mutum ashirin. Gwamna sai da ya ba da kalmar shahada wa mutum talatin zuwa hamsin. Malam Ibrahim Shekakarau sai da ya ba da kalmar shahada wa mutum talatin. Haka maluma su ka rinka ba da kalmar shahada”.

“Bayan an kammala wannan, dukkan waɗanda su ka musuluntan nan, kowacce mace sai da aka ba ta turmin zani aka ba ta jari da za ta yi sana’a. Idan namiji ne sai da aka ba shi turmin shadda aka ba shi jari da zai yi sana’a. Ina so duk Nageriya ku faɗa min gwamnan da ya na kan kujerar gwamna zai zauna ya na musuluntar da jama’a su na karɓar kalmar shahada ?”.

“Ban ce maka bai da laifi ba, ya na da laifuffuka daiwa a wajen Allah, amma ni a wajena duk laifin da ya aikata wannan aikin alherin ya kai ya shafe laifin”.

“Manzon Allah (S.A.W) ya ce ba mutum ɗari biyu ba, mutum ƙwara ɗaya tallintal ya musulunta a sanadiyyarka, ya fi muhimmanci a kan a tara jajayen raƙuman ƙasar saudiyya a ba ka. Mutum ɗaya ya musulunta a nan Kano a sanadiyyarka, wannan musulunci da ka ba shi, ya fi duk motoci jifa-jifai da ke cikin garin Kano”.

“Kun san abin da zai ba ku mamaki ?, a ranar su ka ba da lissafin waɗanda su ka musulunta albarkar hanyar wannan bawan Allah (Gwamna Ganduje), wannan adadin a wannan rana mutum dubu goma sha tara da ɗari biyu da biyu. Gwamna me da’awa”.

“Ba maganar su wa ake cirewa yanar ido ake ba. Masabaƙa da ake ta karatun alƙur’ani mai girma bayan wacce ake a ƙarƙashin ɗan Fodiyo, akwai musabaƙar da ake yi a nan Jiha ƙarƙashin gwamna (Ganduje), wadda a aljihunsa zai ɗauki nauyinta ba a kuɗin gwamnati ba”.

“Wannan ta ƙarshe da aka yi, ina cikin shugabanni masu jawabi a taron da aka yi, na ga abin da ya ban mamaki, mahaddatan Ƙur’ani maza da mata yara ƙanana aka yi musu kyaututtuka na alfarma da girmamawa domin a yi Inkwarejin ɗin su su ƙara haddar al’ƙur’ani mai girma. Faɗa min gwamnan da ya ke yin wannan a Nageriya ?” (Sai Gwamna Ganduje).

“Yanzu Alaramma ya ke faɗa amin bayin Allah da aka taimaka Fisabilillah ciwon makantaka sama da mutum dubu ɗari da tamanin ba sa gani aka buɗe musu ido. Masallatai da aka gina wa ya san iyakar su, makarantu wa ya san iyakar su ? Wanda zai yi wannan aikin (Gwamna Ganduje), mu na yi masa kykkyawan zato. Mai laifi mai laifi ne, mai kura-kurai mai kura-kurai ne, faɗa min gwamnan da bai kuskure a Nageriya, faɗa min gwamnan da bai laifi a Nageriya ?”.

Shaikh Kabir Haruna Gombe, ya yi waɗannan kalamai ne a kan mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje gabanin babban zaɓen shekarar (2019), kwanaki kaɗan bayan sun amsa gayyatar mai girma gwamna wajen Musuluntar da Maguzawa sama da mutum ɗari biyu a wannan lokaci kaɗai.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

Bayan Kammala Ziyarar Aiki A Ƙasashen Waje A Yau Gwamna Ganduje Ya Dawo Gida Nageriya 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Yau Lahadi, 24 ga watan Nobemba, 2019.
Bayan shafe tsawon wasu ƴan kwanaki ya na gudanar da ziyarar aiki a ƙasashen waje, cikin amincewar Allah a yau mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya dawo gida.

Gwamna Ganduje ya samu nasarar halartar taro ne kan sha’anin kiwon lafiya shi da wasu takwarorinsa gwamnoni a ƙasar Amurka. Bayan nan kuma, gwamna Ganduje ya ziyarci ɗaliban Kano da ke ƙasar Faransa waɗanda su ke ƙaratu a ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin gwamnatin Jihar Kano da kuma ƙasar ta Faransa.

Inda kuma ɗalibai su ka bayyana farin cikinsu matuƙa da wannan ziyara ta mai girma gwamna, sannan kuma su ka bayyanata a matsayin wani abin alfahari da zai taimaka wajen ƙara musu ƙarfin gwiwa kan karatun da su ke.

Gwamna Ganduje ba ya gida wata kotu ta yi hukunci kan masu martaba sarakunan Jihar Kano, sannan ba ya nan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar masa da nasarar zama zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano. Cikin ikon Allah a yau mai girma gwamna ya dawo, zai kuma ɗora daga inda ya tsaya kan ɗumbin ayyukansa na bunƙasa cigaban Jihar Kano.

Mu na yi wa mai girma gwamna maraba da dawowa.

Continue Reading

Siyasa

‘Yan sanda sun mikawa Ganduje yaran Kano da aka ceto

Published

on

By

GARKUWA DA YARA A JIHAR KANO: RUNDUNAR ƳAN SANDA TA MIƘAWA GWAMNATIN JIHAR KANO YARA GUDA BAKWAI CIKIN TARAN DA AKA CETO

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Nan Ba Da Jimawa Ba, Za Mu Kira Zama Na Musamman Da Iyayen Da Aka Samu Nasarar Kuɓutar Da Ƴaƴansu Domin Tattaunawa Da Su Da Yaran Gaba Ɗaya. Inji Gwamna Ganduje.

-Tun A shekarar (2016) Aka Sace Min Ɗiyata A’isha, Amma Yanzu Jami’an Ƴan Sanda Sun Gano Min ita, Na Gode Musu, Inji Ɗaya Daga Cikin Iyayen Da Aka Yi Garkuwa Da Ƴaƴansu A JIhar Kano.

-Dazarar Mun Kammala Tattara Bayanai Kan Binciken Da Mu Ke, Za Mu Gurfanar Da Masu Laifin A Gaban Kotu, Inji (CSP) Saje.

Yau Talata, 22 ga watan Octoba, 2019.
Rundunar jami’an tsaro ta ƴan sanda ta ƙasa a Jihar Kano, ta miƙawa gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje yara guda bakwai daga cikin taran da aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane waɗanda aka sace su aka kai su Jihar Anambara aka sayar da su aka kuma sauya musu addini.

Rundunar ƴan sandan sun bayyana cewar yaran sun samu laluri na rashin lafiya, kuma dukkaninsu su na asibiti su na karɓar magani a cikin birnin Jihar Kano.

A ya yin da ya ke karɓar yaran a ɗakin taro mai suna (Africa House) da ke cikin gidan gwamnati, a madadin mai girma gwamna, sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya bayyana gano yaran a matsayin wani gagarumin aiki abin sambarka, inda jami’an tsaro na ƴan sanda su ke ƙoƙari matuƙa wajen yaƙi da ayyukan laifi.

“Ya zama wajibi na yabawa shugaban rundunar ƴan sanda (CP) na Jihar Kano da kuma rundunar jami’an tsaro ta musammam mai yaƙi da masu garkuwa da mutane kan ceto waɗannan yara da su ka yi. Tun bayan faruwar wannan al’amari ƴan sanda su ke ƙoƙarin kulawa da wannan yanayi da aka samu akai ciki domin tabbatar da cewa ba a karya doka da kawo tarnaƙi ga zaman lafiya a kowane wuri ba”. Inji gwamna Ganduje.

“A kan wannan batu, musamman, gwamnatin Jihar Kano ta tuntuɓi sassan hukumomin tsaro saboda halin da aka shiga domin tabbatar da cewar yanayin bai haifar da wani abu marar daɗi ba. Mun himmatu ƙwarai wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma da na gwamnati gaba ɗaya”. Cewar gwamna Ganduje.

“A dai kan wannan batu, ina miƙa ƙorafi ga iyayen da aka ceto yaran nasu da su rika taka-tsan-tsan da dukkan bayanai da kalaman da ake zuzutawa a kafafen watsa labarai daga ɗaiɗaikun al’umma da ƙungiyoyi domin zare kansu da ƴaƴansu daga bayanai da ba su kamata ba, domin wasu su na amfani da wannan dama saboda son zuciyoyinsu. Kuma ana nan an cigaba da gudanar da bincike na zahiri kan wannan batu da sauran batutuwa masu alaƙa. Sannan jami’an tsaro za su ɗauki dukkan matakin da ya dace. Daga nan sai ya buƙaci da su gujewa duk wasu kalamai da ka iya haifar da ruɗani a cikin al’umma”. Inji gwamna Ganduje.

Daga nan kuma sai gwamna Ganduje ya sanar da su tsare-tsaren da ake domin gudanar da ganawa ta musamman a tsakanin gwamnati da yaran da aka ceto da kuma iyayensu gaba ɗaya zuwa nan gaba kaɗan cikin ranar da za a sanar.

A ya yin miƙa yaran ga mai girma sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, a madadin mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kwamandan rundunar ƴan sanda ta musamman kan yaƙi da masu garkuwa da mutane na Jihar Kano, (CSP) Babagana Saje, ya yi bayani cewa, ya tura jami’ai domin kamewa tare da gano mafakar waɗanda ake zargi da garkuwa da mutanen a Jihar Kano da Onisha.

“Mun kame tare da tsare wasu daga cikin waɗanda ake zargin ciki har da wani da matarsa waɗanda su ka saci yaran a nan su ka je su ka sayar da su a Onisha. Sun sayar da yaran ne a kan kuɗi naira (200,000), ya yin da ita kuma matar a Onisha ta sake sayar da yaran ga abokan hulɗarta a Jihar Legas. A taƙaice, biyu daga cikin yaran mun gano su ne a tattare da ita a matsayin bayi masu yi mata aikace-aikace a cikin gida.

Sannan kuma jami’an ƴan sandan sun gano cewa yaran da aka sace an sauya musu addini daga Musulunci zuwa Kiristanci, an kuma sauya musu haƙiƙanin yadda su ke tun asali.

Kamar yadda (CSP) Saje ya bayyana, “iyaye bakwai sun gane ƴaƴansu bayan ɗaukar matakin bin tsari irin na tsaro. Amma har yanzu akwai biyu da su ke iƙirari. Dan haka mu na umartar iyayen da aka sace musu yara a Kano da su daure su zo ofishinmu domin tantance sauran yara biyun da su ke hannunmu”.

Daga nan kuma sai ya ba da tabbacin gurfanar da duk waɗanda ake zargi da satar yaran a gaban kotu nan gaba kaɗan da zarar sun kammala binciken da su ke.

Da ya ke gabatar da jawabi a madadin iyayen yaran Mallam Muhammad Ali, ya yi bayani cewa tun shekarar (2016) aka sace masa tasa ɗiyar (A’isha). Kuma dukkan iyaye sun yi farin ciki da aka gano musu ƴaƴansu. Daga nan kuma sai ya yabawa jami’an tsaron rundunar ƴan sanda tare da gode musu dangane da wannan gagarumin aiki da su ka ka yi.

Continue Reading

Labarai

Gwamna Ganduje zai kara karfafa hurdar jihar Kano da kasar Faransa

Published

on

By

GWAMNA GANDUJE ZAI ƘARA ƘARFAFA DANGANTAKAR HULƊAR KASUWANCI DA AL’ADU A TSAKANIN JIHAR KANO DA KUMA ƘASAR FARANSA

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ƙasar Faransa Ta Shiryawa Gwamna Ganduje Taron Tattaunawa A Tsakaninsa Da Bankin Haɓaka Tattalin Arziƙi Na Ƙasar Faransa Domin Kawo Cigaba Jihar Kano.

-Jakadan Ƙasar Faransa A Nageriya, Ya Yabawa Ƙoƙarin Gwamna Ganduje Wajen Kyautata Fannin Ilimi Da Sauran Fannoni A Gwamnatinsa.

Yau Talata, 22 ga watan Octoba, 2019.
A ƙoƙarinsa na cigaba da haɓaka tattalin arziƙin Jiha da kuma cigaba da kyautata dangantakar tattalin arziƙi da sauran ƙasashen Duniya, an tsara mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai kai wata ziyarar aiki zuwa ƙasar Faransa inda zai gana da manyan ƴan kasuwa na ƙasar domin jawo hankalin masu zuba jari wajen ƙara ƙarfafa dangantakar tattalin arziƙi da ta al’adu a tsakanin Jihar Kano da kuma ƙasar ta Faransa.

Daga cikin ginshiƙan ziyarar tasa, har da batun ganawa ta musamman tare da ɗalibai ƴan asalin Jihar Kano waɗanda su ke karatu a ƙasar ta Faransa a cikin jami’o’i daban-daban na ƙasar inda wasu su ke matakin digiri na biyu wasu kuma su na matakin digirin-digirgir.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a ya yin da ya ziyarci ofishin jakadancin Faransa da ke Abuja inda ya gana da jakadan ƙasar Mista Jeremo Pasquier a wannan rana ta Talata, inda kuma ya ba shi tabbacin yin iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya samo gagarumar nasara kan tattalin arziƙin Jihar Kano wajen ganawa da manyan ƴan kasuwa na ƙasar ta Faransa dazarar ya je.

A wannan zango mulki nasa na biyu, gwamna Ganduje ya bayyana cewa zai yi aiki tuƙuru wajen ganin jihar Kano ta zama mashigar ƴan kasuwa na duniya masu zuba jari. “A yunƙurinmu na kyautata tattalin arziƙin Jiharmu, za mu cigaba da haɗa hannunmu da sauran ƙasashen duniya kamar Faransa kan tattalin arziƙi da kuma al’adu”. Inji Gwamna Ganduje.

Dangane da kyautata dangantakar al’adu, a cewar gwamna Ganduje, a lokaci guda, zai zama wata hanya ta ƙara kyautata sha’anin tsaro da kuma zaman lafiya a Duniya, inda ya yi ƙarin bayani da cewa: “Tare da daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin Jihar Kano da ƙasar Faransa, ziyarata zuwa ƙasar za ta zama wata babbar dama ce ta ƙara ƙarfafa dangantakar wacce za ta kasance har abada”. Cewar Gwamna Ganduje.

“Sannan zan yi amfani da wanna dama wajen yin godiya ga ƙasar Faransa dangane da damar tallafin karatu da ku ka ba wa matasanmu da kuma malamanmu na manyan makarantun gaba da sakandire”. Inji gwamna Ganduje.

Inda daga nan kuma gwamna Ganduje ya ƙara da cewa ganawar da zai yi da ɗalibai ƴan asalin jihar Kano da ke karatu a ƙasar ta Faransa, zai taimaka wajen ƙara sanyawa ɗaliban ƙarsashi da himmar cigaba da maida hankali kan karatunsu.

Daɗi da ƙari, gwamna Ganduje zai yi amfani da ziyarar wajen gabatarwa da ƙasar ta Faransa halin da ake ciki dangane da gudunmawar kuɗaɗe da ta ba wa Jihar Kano a baya domin inganta fannin samar da ruwan sha a Jihar Kano.

Kamar yadda ya bayyana, “mun yi amfani da damar wajen kyautata aikin samar da ruwa, wadda kuma babu wata gagarumar matsala tun (1928) lokacin da aka ƙirƙiro ta har zuwa yau. Wannan kyautatawa da mu ka samu daga gwamnatin Faransa ta zama wani abin alfahari a gare mu”.

Bayan gyara aikin samar da ruwan sha, gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin Jiha ta ƙara ƙaimi wajen ƙara kyautata hanyoyin samar da ruwan, inda ya yi ƙarin haske da cewa: “mu na yin duk mai iyuwa iya bakin ƙoƙarinmu domin ganin cewar mun kyautata sha’anin samar da ruwan sha kamar yadda mu ka fara cikin juriya da jajircewa”. Gwamna Ganduje ya bayyana.

“Ina mai farin cikin shaida muku cewa, mu na gudanar da gagarumin aiki da kyautatawa a fannin samar da ruwan sha. Kamar yadda mu ke yi a sauran fannoni a Jihar Kano”. Inji Gwamna Ganduje.

A ya yin da ya ke maida jawabi, jakadan ƙasar ta Faransa a Nageriya, Mista, Pasquer, ya yabawa gwamna Ganduje kan yadda ya ke kykkyawan aiki tuƙuru a fannin ilimi da kuma sauran fannoni a gwamnatinsa.

Daga nan kuma sai ya ƙara da ba da tabbacin ƙasarsu ta Faransa wajen cigaba da marawa gwamnatin Jihar Kano baya kan fannin ilimi da kuma tabbatar da kykkyawar alaƙar dangantakar tattalin arziƙi a tsakanin ƙasar da kuma Jihar Kano.

A ƙoƙarin kyautata dangantakar tattalin arziƙin daga dukkan sasannin cigaba, Jakada Pasquier ya bayyana cewa, “akwai shiri da aka yi inda mai girma gwamna zai gana da bankin haɓaka tattalin arziƙi na ƙasar Faransa da zarar ya samu isa can. Wannan zai ɗauke mu hanya mai tsawo wajen kyautata alaƙar dangantakarmu”.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending