Connect with us

Labarai

Yadda gwamna Ganduje ke kokari kan tsaro a Kano

Published

on

ƘOƘARIN GWAMNA GANDUJE KAN SASHEN TSARO GAGARUMAR NASARA CE ABAR KOYI GA SAURAN GWAMNONI

SHARHI: Bashir Abdullahi El-bash

Yau Laraba, 30 ga watan Octoba, 2019.
A matsayinsa na mutumin da ya san muhimmancin zaman lafiya a tsawon rayuwarsa gaba ɗaya kan ayyukan gwamnati da jama’a, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ko kaɗan ba ya wasa ko sakaci da dukkan al’amuran da su ka shafi tsaro.

Kafin zamansa zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano a shekarar (2015), Jihar ta fuskanci manyan ƙalubale da tarnaƙin matsalar tsaro, tayadda kuma hakan ya zama silar jefa rayuwar al’umma cikin hatsari.

Alal misali, ƴankuna da dama na Jihar sun fuskanci matsaloli da hare-haren ƴan daba da kuma ƴan fashi da makami da masu haurawa gidajen jama’a su na yi wa mata fyaɗe.

Ba tare da ɓata lokaci ba, da zuwan mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano, ya haɗa kai da dukkan sassan hukumomin jami’an tsaro inda ya samar da managartan tsare-tsaren da su ka taimaka wajen magance ayyukan laifi da kaso mai girma a loko da saƙo na Jihar.

Tsarin gwamna Ganduje kan sha’anin tsaro ya samar da tsare-tsare masu inganci kan kyautata ƙwarewar jami’an tsaro da kuma tallafawa sassan hukumomin tsaron da kayan aiki irin na zamani domin yaƙi da masu aikata laifuffuka.

A wannan sharhi, ina cike da fatan gabatar da bayanai kan yadda wannan ƙoƙari na gwamna Ganduje ya taimaka wajen ƙarfafar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano domin cimma burin da ake da shi na cigaba da haɓaka tattalin arziƙin Jihar da ma ƙasa gaba ɗaya.

Gwamna Ganduje ya samar da manyan na’urori irin na zamani ga jami’an tsaro kan kuɗi kimanin (Naira Miliyan 500)

Sanin kowa ne an fuskanci ƙalubale da matsalolin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, kuma masu laifin sun maida Jihar Kano tamkar wani sansanin yada zango ko mafakar fakewarsu, sai dai tuni an gano su an kuma kame su.

Al’ummar Jihar Kano sun shiga mamaki da tambayoyin mai ya sa dukkan manyan masu laifi ake kama su a Jihar Kano ?

Amsar waɗannan tambayoyi ta na tattare ne da waɗannan manyan na’urorin bincike da bin diddigi irin na zamani da gwamna Ganduje ya samar a kan kuɗi kimanin (Naira Miliyan 500).

Kamar yadda gwamna Ganduje ya bayyana, waɗannan na’urori na zamani, su na da damar sanin bayanai kan kiran waya har na tsawon shekaru biyu, inda ya ƙara da cewa har da ɗumbin makamai duk an gano, sannan an kuma kame masu aikata satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Daɗi da ƙari, na’urorin bin diddigin ba wai a iya Jihar Kano kaɗai ya samar da su ba, ya haɗa yankin Arewa maso Yamma ne gaba ɗaya. Tayadda hakan kuma wata alama ce da ke ƙara shaida shugabanci nagari abin misali daga gwamna Ganduje ba ga iya jiharsa kaɗai ba a duk Nageriya gaba ɗaya.

A ya yin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Barista M.A Lawal a gidan gwamnatin Jihar Kano, gwamna Ganduje ya labarta musu cewa na’urar bin diddigin, ta taimaka matuƙa wajen kame manyan masu garkuwa da mutane a Jihar

A cewar gwamna Ganduje, daga cikin manyan masu garkuwar da aka samu nasarar cafkewa, akwai waɗanda su ka yi garkuwa da mai girma Magajin Garin Daura, da kuma waɗanda su ka yi shirin yin Garkuwa da mataimakin gwamnan Jihar Nassarawa. Da kuma riƙaƙƙen mai garkuwa da mutane na Jihar Taraba, Hamisu Bala Wadume, duk an kama su ne da taimakon wannan nau’urar bin diddigi ta zamani da gwamna Ganduje ya samar.

“Wannan na’urar bin diddigi ta na gudanar da kykkyawan aiki na ban mamaki. Tsaro ya kyautata matuƙa. Kuma nan gaba kaɗan za mu ƙaddamar da fara amfani da na’urar naɗar bayanai (CCTV) a duk faɗin Jihar domin ƙara kare Jiha. Dangane da bayananku tsare-tsare da dama za su bayyana kan cigaba da kare al’umma”.

Taro na musamman kan sha’anin tsaro nan gaba kaɗan:

Sannan kuma, a saboda nasarorin da aka cimma wajen amfani da ƴan sandan al’umma, gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta shirya taro na musamman kan wannan batu nan gaba kaɗan.

“Nan ba da jimawa ba, za mu shirya taro na musamman dangane da batun ƴan sandan cikin al’umma. Ina ba ku tabbacin za ku kasance cikin taron. Kuma za ku kasance cikin al’umma masu amfani a gare mu. Na fahimci cewa ku na da maida hankali na musamman kan tsaro a wannan ƙasa tamu, ba shakka wannan abin yabawa ne.

“Wannan nasara da mu ka samu a wannan wuri, Allah ne ya ba mu biyo bayan sanadin haɗin kai da gudunmawar da kowa ya bayar daga ɓangaren al’umma da kuma sassan hukumomin tsaro”.

“Babu wani ƙoƙari da zai yi yawa, dan haka, tsaro shi ne muhimmin abun da mu ka sanya a gaba. Da taimakon Allah mu na da manyan abubuwa biyu da za su taimaka mana wajen cigaba da kare wannan matakin farin ciki da mu ke ciki kan amincin Jiharmu a bar alfaharinmu”.

“Ƴan sandan cikin al’umma na daga cikin manyan tsare-tsaren da su ka taimakawa Jihar. Inda ya bayyana yadda aka samar da kykkyawar alaƙa a tsakaninsu da kuma dukkan sassan hukumomin tsaro”.

“Jami’an tsaronmu su na aiki hannu da hannu domin cigaba da samar da tsaro a Jihar Kano. Kuma babu wata rashin jituwa a tsakaninsu. Domin sun yi imanin su na da rawar takawa gaba ɗaya wajen ɗorewar zaman lafiya a muhallinmu.

Gwamna Ganduje Ya Goyi Bayan Sabon Tsarin Rijistar Baƙi Ƴan Ƙasashen Waje Ƙarƙashin Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙasa (NIS):

Gwamna Ganduje ya yi tsokaci game da sabon tsarin yi wa baƙi ƴan ƙasashen waje Rijista ƙarƙashin hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) inda ya bayyana cewa tsarin ya zo a daidai kan gaɓa domin gano yawan mutanen da ke haurowa zuwa Nageriya ba bisa ƙa’ida ba.

“Mu na da buƙatar amfani da kimiyya cikin rayuwarmu, musamman ma a kan sha’anin tsaro. Wannan ya shaida mana ƙarara yadda hukumar shige da fice ta ƙasa ta kai mu zuwa ga mataki nagaba a ƙarƙashin shugabancin Muhammad Babandede”.

Gwamna Ganduje wanda ya halarci taron ƙaddamar da rijistar a harabar makarantar horas da jami’an hukumar shige da fice ta ƙasa (Immigration Training School) da ke Jihar Kano. Ya hori baƙi ƴan ƙasashen waje da ke Jihar Kano da su maida hankali wajen yin rijistar.

“A yanayin ɗabi’ar baƙi na Kano, za ta ba su damar maida hankali matuƙa kan yawan baƙin da ba ƴan asalin ƙasa ba ne, kamar yadda ya ke cewa”.

“Ya zama wajibi a maida hankali yadda ya kamata. Ina mai jan hankali da kira ga dukkan waɗanda ba ƴan ƙasa ba ne da su hanzarta zuwa a yi musu rijista”.

“Samun cikakken bayani game da adadin yawan baƙi ƴan ƙasashen waje, wata tabbatacciyar hanya ce wacce za ta taimaka wajen kare Jiha da ƙasa gaba ɗaya. Za mu ba da dukkan haɗin kai da kuma goyon bayan da ake da buƙata waje samun nasarar wannan sabon tsari”.

“Mu na cikin farin ciki tare da alfahari da shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa, Muhammad Babandede kan wannan sabon tsari da ya samar ƙarƙashin ɗaukwar nauyin hukumar. Wannan yunƙuri ne na kishin ƙasa da kuma ƙarfafa gwiwar kowane sashe”. Inji Gwamna Ganduje.

Gwamna Ganduje Ya Ba Da Kuɗi Kimanin (Naira Miliyan 318) Kan Cibiyar Horas Da Sojoji A Dajin Falgore:

Ƙaramar hukumar Doguwa a Jihar Kano na daga cikin ƙananan hukumomin da aka haƙƙaƙe cewar na daga cikin mafakar masu aikata laifuffuka saboda tafkeken dajin nan na Falgore da Allah ya azurta ta da shi inda kuma a nan ne masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma ɓarayin shanu su ke fakewa.

A saboda wannan dalili ne kuma, hukumar sojin ƙasa ta kafa wata cibiya ko kuma sansanin horas da jami’anta na soji. Domin daƙile dukkan wani tanadin masu aikata laifuffuka.

A cikin watan Yuni na wannan shekarar, gwamna Ganduje ya ba da gudunmawar kuɗi kimanin (Naira Miliyan 318) domin gyarawa sojoji dajin da kuma samar musu kayan amfanin yau da kullum.

Gwamna Ganduje ya sanar da batun ba da wannan gudunmawa ne ya yin bikin rundunar soji bataliya ta ɗaya a Barikin Bakabu da ke Jihar Kano.

Inda ya ƙara da cewa jami’an sojin da za a horar a wannan daji, za su taimaka wajen yaƙar ɓarayin mutane da ɓarayin shanu da ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuffuka.

“Mun ba da gudunmawa kan wannan muhimmin aiki, domin zai taimaka mana wajen yaƙi da ƙalubalen tsaro a yankin”.

Gwamna Ganduje ya kuma jaddada batun samar da kykkyawan tsari kan ƴan sandan cikin al’umma, domin shigar da kowa cikin shirin samar da tsaro.

“Tuni mun fara wannan yunƙuri wajen shigar da limamai da masu unguwanni da sauran masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar ƙaraye, nan gaba kaɗan za mu sake gudanar da wani a masarautar Rano”.

Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa, gwamnatin Jiha za ta gudanar da taro da masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Tudun Wada yankin dajin Falgore.

Gwamna Ganduje Ya Kuma Kashe (Naira Miliyan 400) kan ayyukan samar da ofisoshin ƴan sanda:

A cikin watan Mayun shekarar 2018 gwamnatin gwamna Ganduje ta amince da kashe kuɗi kimanin (Naira Miliyan 400) domin gina sabbin matsugunnin ƴan sanda a wasu sassa na Jihar Kano.

Manufar aikin ita ce kakkaɓe masu laifi da kuma ƙarfafar ƴan sandan cikin al’umma.

Ayyukan sun haɗa da ofisoshin ƴan sanda guda biyu a titin kotu da ke ƙaramar hukumar Tarauni da Tudun Wada a kan kuɗi kimanin naira miliyan 123,364,230. Sai kuma wata a Fanshekara yankin ƙaramar hukumar Kumbotso a kan kuɗi naira 59,589,240. Da kuma wasu biyun a Rijiyar Zaki da Zango da ke a ƙaramar hukumar Ungogo a kan kuɗi naira miliyan 101,841,438.50.

Sauran sun haɗa da ofisoshin ƴan sanda a titin kotu ƙaramar hukumar Tarauni da kuma Fire Brigade outpost a Dakata da ke ƙaramar hukumar Ungoggo a kan kuɗi naira miliyan 71, 626, 643. 58.

Haka zalika an amince da gina wani ofishin ƴan sandan a garin Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, da kuma gina gidajen ƴan sanda guda goma sha biyu a birnin Kano.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a ya yin aza harsashin ofishin ƴan sanda na titin kotu da ke ƙaramar hukumar Tarauni. Inda daga bisani kuma gwamna Ganduje ya miƙa gudunmawar ababen hawa da wasu kayan aiki ga rundunar ƴan sandan Jihar Kano.

A ya yin taron, tsohon shugaban rundunar ƴan sanda na ƙasa, Ibrahim Idris ya yaba wannan ƙoƙari na gwamna Ganduje kan ƙarfafar ayyukan ƴan sanda. “Jihar Kano a yau ta zama abar kwaikwayo ga sauran Jihohi, ya kyautu a yi koyi da ita kan yadda ta ke goyon bayan ƴan sanda”.

Babu ko shakka, wannan ƙoƙari na mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje babban jagoran tsaron Jihar Kano, ya zamar da jihar Kano cikin aminci da zaman lafiya a Nageriya. Ya kuma kyautu sauran Jihohi su yi koyi da irin tsare-tsaren da gwamna Ganduje ya samar kan kyautata tsaro a Jihohinsu.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Majalissar Zartarwa Ta Amince  A Kafa Ƙarin Masarautu Guda Huɗu U A Jihar Kano 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Kuma Tuni Ta Tura Ƙudirin Dokar Zuwa Gaban Zauren Majalissar Dokoki Na Jihar Kano.

Yau Litinin, 2 ga watan Disamba, 2019.
A wani zama da ta gudanar a daren Jiya Lahadi, majalissar zartarwa ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da ƙudirin dokar kafa ƙarin masarautu guda huɗu a Jihar Kano. Waɗanda su ka haɗa da masarautar: Bichi da Gaya da Rano da kuma Ƙaraye. Inda tuni kuma majalissar ta tura ƙudirin dokar zuwa gaban zauren majalissar dokoki na Jiha.

Sanarwar da aka fitar daga gidan gwamnati, ta kuma ƙara yin bayani da cewa dama can akwai wasu daga cikin waɗannan masarautu tun shekarun baya masu tsawo da su ka wuce, juyin zamani ne ya nemi ya shafe tarihinsu, kuma ko a zamanin janhoriya ta biyu sai da aka nemi a farfaɗo da su, amma aka samu tsaiko.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa majalissar zartarwa ta tattauna sosai game da alfanun ƙarin nasarautun kafin ta cimma wannan matsaya da ta ɗauka, ta kuma fahimci cewa ƙarin masarautun zai taimaka sosai wajen ƙara kusanci a tsakanin al’umma da sarakunan gargajiya. Sannan kuma ƙarin masarautun zai taimaka matuƙa wajen ƙara haɓaka harkokin kasuwanci da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Kano cikin hanzari.

Haka zalika, ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na ilimi kyauta kuma wajibi tun daga firamare har zuwa babbar sakandire, ya na buƙatar taka rawar al’umma sosai da sosai musamman ma sarakunan gargajiya domin samun nasarar shirin. Dan haka ƙarin masarautun zai taimaka sosai da sosai wajen cimma wannan buri.

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa ƙudirin dokar da aka ɗabbaka a zauren majalissaar dokoki a 2019, kotu ta rushe shi ne saboda mutum ne daga cikin al’umma ya gabatar da shi ba ɗaya daga cikin ƴan majalissa ba.

Kamar yadda sanarwar ta ƙara, majalissar zartarwar ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta kuma buƙaci zauren majalissar dokokin na Jihar Kano da su yi duba da buƙatun al’umma wajen amincewa da ƙudirin dokar.

Continue Reading

Labarai

Gwamna Ganduje Ya Taya Mallam Ibrahim Shekarau Murnar Samun Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-“Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa Da Aka Ba Wa Sanata Shekarau Alama Ce Da Ke Ƙara Shaida Yadda Duniyar Ilimi Ta Gamsu Da Irin Ɗumbin Gudunmawar Da Ya Ba Ta A Zamanin Da Ya Riƙe Matsayin Gwamna Da Muƙamin Ministan Ilimi Na Nageriya”. Inji Gwamna Ganduje.

Yau Asabar, 30 ga watan Nobemba, 2019.
Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano hawa biyu, kana kuma sanata mai ci, Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano murnar samun lambar yabo ta digirin girmamawa wanda Jami’ar Ritman da ke birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom ta ba shi a wannan rana ta Asabar.

Digirin girmamawar wacce jami’ar ta ba shi saboda irin ɗumbin gudunmawar da ya bayar a fannin iilimi a zamanin ya na matsayin gwamna da matsayin ministan ilimi, gwamna Ganduje ya taya shi murna a madadin gwamnatin Jihar Kano da al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya.

Kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar taya murnar da gwamna Ganduje ya bayar, “mai girma gwamna ya ga lambar yabo ta digirin girmamawa da aka ba wa Sanata Ibrahim Shekaru, inda lambar ke ƙara shaida yadda fannin ilimi ya gamsu da irin ɗumbin nasarori da gudunmawar da ya bayar a fannin da kuma gina rayuwar ɗan adam a lokacin da ya riƙe matsayin gwamna da kuma Ministan Ilimi a Nageriya.

Idan za a iya tunawa, ko a shekarar 2009, Sanata Shekarau ya samu irin wannan lambar yabo ta digirin girmamawa daga Jami’ar ƙasa ta Nsuka”. Sanarwar ta bayyana.

Inda kuma gwamna Ganduje ya ƙara da cewa wannan lambar yabo ga sanata Shekarau tambar ƙara zaburar da shi ne ya ƙara himma da ƙoƙari kan ƙoƙarin da ya ke na ba da gudunmawa wajen gina ƙasa da kuma gina rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Ya yin da ya ke taya Sanata Shekarau murnar wannan ƙarin matsayi da ya samu, gwamna Ganduje ya yi masa fatan alkhairi tare da fatan ya ƙara cigaba da dagewa wajen ba da gudunmawa kan cigaban ƙasa da sauran jama’a.

Continue Reading

Labarai

JAMI’AN TSARO SUN SAMU NASARAR KAME WANDA YA SHIRYA AURAR DA FATIMA GANDUJE TA BOGI

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ya Samar Da Fatima Ganduje Ta Bogi Ya Karɓi Kuɗi Kimanin Naira Miliyan Biyar Da Sunan Zai Ba Da Auren Fatima Ganduje Ta Gaske.

-Iyalan Gwamna Ganduje Sun Ba Da Umarni Jami’an Tsaro Su Cafke Duk Wani Ko Wata Da Za Su Bayyana Kansu A Matsayin Yaran Gidan Su Damfari Al’umma.

Yau Asabar, 23 ga watan Nobemba, 2019.
Jami’an tsaro sun samu nasarar kame wani matashi mai suna Abdullahi Zakari, wanda ya bayyana kansa a matsayin yaron gidan mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya damfari wani mutum mai sana’ar saida magunguna mai suna Alhaji Bashir Amadu Usaini da ke unguwar Tudun Yola zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan Biyar da sunan wai zai haɗa shi da ƴar mai girma gwamna Fatima Ganduje ya aura.

Yadda lamarin ya faru shi ne: tun kafin Fatima Ganduje ta yi aure, Abdullahi Zakari ya samu wani mai suna Alhaji Bashir Amadu ya kwaɗaita masa cewar shi yaron gidan gwamna Ganduje ne, dan haka ya yi masa alƙawarin zai haɗa shi aure da Fatima Ganduje. Sannu a hankali har ta kai ga wannan ɗan damfara (Abdullahi Zakari) ya samar da Fatima Ganduje ta ƙarya ya haɗa su da Alhaji Bashir Amadu su na waya da juna da sunan soyayya.

Sannu-sannu har ta kai ga wannan Fatima ta bogi ta na neman kuɗi a wurin Alhaji Bashir Amadu inda ta ke shaida masa cewar wai auren dole za a yi mata a gida, dan haka ba ta tambayar kowa kuɗi in ba shi ba, saboda shi ta ke so ta aura.

Sannan kuma, shi wannan ɗan damfara ya samar da wata matar ta bogi a matsayin Balaraba Ganduje, wato yayar Fatima Ganduje, ta yadda duk kuɗin da Fatima Ganduje ta bogi za ta nema a wurin Alhaji Bashir Amadu, ita wannan Balaraba Ganduje ta bogin ce ta ke ƙara ba shi tabbacin da ƙarfin gwiwa kan ya ba da ko nawa ne ta tambaye shi saboda wai ita Fatiman ba ta tambayar kowa kuɗi a gidan nasu sai shi saboda shi ne ta ke son zai aure ta, wanda hakan ne kuma ya ke sanya shi ko da yaƙi ko kuma ba shi da kuɗi a lokacin to wannan ƙaimi da Balaraba Ganduje ta bogin ta ke yi masa kan sa shi ya nemo ya bayar.

Bayan haka, shi dai wannan ɗan damfara, har Gwaggo wato Hajiya Gafsat Ganduje ya samar ta bogi, inda ya sanya ita waccar Fatiman bogin ta nemi wayar mahaifiyar shi wanda ake damfara ɗin, Bashir Amadu ta haɗa su da wannan Gwaggo ta bogi su ka gaisa da mahaifiyarsa a lokacin da ba ta da lafiya.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da Fatima Ganduje da Balaraba Ganduje da kuma (Gwaggo) Hafsat Ganduje duk na bogi kafin Fatima Ganduje ta gaske ta yi aure har tsawon kusan shekaru uku.

Sannan bayan Fatima Ganduje ta gasken ta yi aure, duk da haka ba su ƙyale shi ba, wannan Fatima Ganduje ta bogin ta cigaba da yi masa waya ta na faɗa masa cewar ita fa ba zaman auren nan za ta yi ba domin dole aka yi mata dan haka za ta kashe auren ta fito ta aure shi.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da waɗannan mata a matsayin ƴaƴa ne na gwamna, wato Fatima da Balaraba, da kuma mahaifiyarsu Gwaggo ya yi ta karɓan kuɗi a hannun wannan bawan Allah mai suna Bashir Amadu Usaini har kimanin Naira Miliyan Biyar cikin shekaru uku da su ka shafe.

Sai dai jami’in tsaro sun samu nasarar kame wannan ɗan damfara, har ma an gurfanar da shi a gaban kotun Noman Salak da ke nan Jihar Kano a jiya, kuma alƙali ya tura shi zaman gidan kaso kafin a nemo sauran matan da ya yi amfani da su wajen shirya wannan damfara da zamba a dawo a cigaba da shari’ar.

Sannan kuma tuni iyalan mai girma gwamna sun ba da gargaɗi kan a guji yarda da duk wani wanda zai je wa da wani da irin wannan alaƙa, sannan kuma duk wanda aka kama to ayi gaggawar sanar da jami’an tsaro mafi kusa domin su kame shi.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending