Connect with us

Nasarorin Ganduje

Yadda gwamna Ganduje ya zamanantar da jihar Kano

Published

on

WAIWAYE ADON TAFIYA JIHAR KANO A ZAMANIN GWAMNA GANDUJE (34)

TSARAWA DA GABATARWA Bashir Abdullahi El-bash

-Cikakken Jawabin Mai Girma Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, A Ranar Rantsuwar Kama Aiki, Kan Wa’adin Zangon Mulki Na Biyu, Laraba, 29 Ga Watan Mayu, 2019, A Filin Wasa Na Tunawa Da Marigayi Janar Sani Abach Da Ke Ƙofar Mata.

Yau Asabar, 26 ga watan Octoba, 2019.
A cigaba da waiwayen baya kan al’amuran da su ka shafi mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatinsa, a yau na yi duba ne ga jawaban da mai girma gwamna ya yi a ranar da aka rantsar da shi kan wa’adin zangon mulki na biyu.

“Yau na sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano a wa’adi na biyu. Wannan nasara ce daga Allah da kuma goyon bayan al’ummar Jihar Kano. Yau Ƙaddara ta, ta sake zama gwamnan Jihar Kano ta tabbata.

Idan za ku iya tunawa, a ranar da na sha rantsuwar kama aiki a wa’adi na farko, ranar 29 ga watan Mayu, 2015, na fara gabatar da manufofina da tsare-tsarena waɗanda na gabatar cikin jawabin da na yi. Inda na yi hasashen kammala ayyukan da gwamnatocin baya su ka fara ba su kai ga kammalawa ba, gami kuma da ƙirƙiro sabbin ayyuka da tsare-tsaren da za su taimaka wajen cigaban al’umma domin gina Jihar Kano, abar alfaharinmu.

A dunƙule za mu tunkari ƙalubalen da ke gabanmu na mayar da Jihar Kano muhalli mafi daɗin rayuwa. Ka da mu manta, zaɓe ya kammala, yanzu abin da ke gabanmu shi ne aiki tare kowa ya ba da gudunmawarsa. Zan tafiyar da gwamnati a buɗe, babu wani wanda za mu watsar, yanzu ba maganace ta jam’iyya ba, Jihar Kano za mu yi wa aiki domin amfaninku.

A shekara hudu, mun shaidawa al’ummarmu ayyukan raya ƙasa da mu ka aiwatar a duk faɗin wannan Jiha. Musamman ayyukan tituna sun mamaye dukkan manyan birane a sassa daban-daban na wannan Jiha.

MANUFOFINMU A MATAKI NAGABA NEXTLEVEL

A matsayin gwamnati, mu na da kykkyawan ƙuduri kan abubuwa da za mu tsara mu aiwatar a cikin shekaru huɗu (4) masu zuwa. Za mu himmatu wajen gina Jiha mai cike da kiwon lafiya mai inganci, da tsarin Ilimi mai nagarta, da kuma fannin noma da raya birane da karkara da samar da ƙarin guraben ayyukan yi, da inganta sha’anin tsaro da na tattalin arziƙi.

(1). ILIMI

Tun a farkon jawabin da na yi biyo bayan samun wannan nasara, gwamnatina za ta fara bayar da ilimi kyauta tun daga Firamare har zuwa babbar sakandire. Kuma za mu cigaba da ingantawa da bayar da tallafi mai gwaɓi a manyan makarantun gaba da sakandire. A yau ina mai tabbatar muku, mun zamar da Ilimi kyauta a kowane mataki ga duk mutane masu buƙata ta musamman (Naƙasssu) tun daga Firamare har zuwa babbar sakandire. Daga baya za mu gabatar da cikakken bayani da tsari kan wannan dama da mu ka bayar ta (Ilimi kyauta).

(2). KIWON LAFIYA

Wannan gwamnatin tamu, za ta samar da cibiyar kula da masu cutar kansa a tsakanin al’ummarmu musamman mata. Domin a sanadiyyar rashinta, al’umma da dama su kan shiga matsanancin hali a duk shekara sanaɗiyyar ƙarancin tsarin kula da cutar kansar da su ke fama da ita.

Mun amince a gina cibiyar kula da masu cutar kansa, mun kuma bayar da kwangilar wannan aiki a kan kuɗi kimanin (Naira Billiyan 2.4) domin yin aiki irin na zamani a cikin (Muhammadu Buhari Specialist Hospital), samar da cibiyar shi ne abu na farko a duk wani asibitin gwamnati.

Gwamnatinmu za ta samar da ma’aikatar ba da gudunmawa da kuma kula da kiwon lafiya a duk sassan wannan Jiha domin cigaba da ɗabbaƙa ayyukan jinƙan al’umma marasa galihu a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu.

(3). SAMAR DA RUWAN SHA

Tsarinmu na samar da ruwan sha, za mu cigaba kan tsarinmu na shekaru (5) na gina fannonin samar da ruwan sha. Kan dokar samar da ruwan sha da ta tsaftar muhalli da ta gabata, za mu tabbatar da mun kammala duk wani aikin samar da ruwan sha ƙarƙashin ma’aikatar samar da ruwan sha domin cigaba da ɗaga darajar Jihar Kano ta hanyar canza sunan ma’aikatar samar da ruwan sha gami da cinikayyar ruwan.

Sunan sabon kamfanin samar da ruwan shan zai zama ƙaramar ma’aikatar samar da ruwan sha ta Jihar Kano, wato “Kano State Small Town Water Supply Agency”. (RUWASA) domin cigaba da samar da ruwan sha ta yadda jama’arta ba za su haura mutum (2,000) ba.

A ƙoƙarinmu kan fannin samar da aikin haɗin gwiwa, gwamnatin Jiha ta samar da Naira (Miliyan 64.5) na kuɗin Yuro daga ma’aikatar Faransa, wanda majalissar tarayya ta amince da kuma majalissar zartarwa ta tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, yanzu haka dukkan tsare-tsare sun kankama domin ƙaddamar da fara wannan aiki a wannan shekara.

(4). FANNIN NOMA

A ƙoƙarinmu na tallafawa matsakaita da ƙananan manoma, gwamnatinmu ta samar da muhallin haɗaka da masu ruwa da tsaki daban-daban domin ciyar da fannin noma gaba.

Shirin babban bankin Duniya kan tallafawa harkokin noma na tsawon shekara biyar ya fitar da (Naira Miliyan 700) domin tallafawa matsakaita da ƙananan manoma

Shi ma Bankin Musulunci ya fitar da ($500 million) domin ƙaddamar da shirin tallafawa harkokin noma don rage raɗaɗin talauci da kuma wadata ƙasa da abinci da kuma samar da tsaro.

A yunƙurinmu na inganta noman auduga a wannan Jiha, gwamnatinmu ta shirya kashe (Naira Biliyan 1.89) kan tanadin shekaru huɗu a ƙananan hukumomi kimanin (32) da aka zaɓa. Domin ƙara yawan abin da ake samarwa.

(5). YAƘI DA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN ƘWAYOYI

A ƙoƙarinmu na yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi musamman a tsakankanin matasa, a lokutan baya mun kashe Miliyoyin Naira kan daƙile matsalar miyagun ƙwayoyi.

A ƙoƙarinmu na kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya, yanzu haka mun kammala duk wasu shirye-shirye na gina ma’aikatar bincike da kulawa gami da yaƙi da matsalar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, za kuma mu meƙa ƙudurin dokar ga masu girma ƴan majalissar dokoki na Jiha domin duba akai.

(6). MASU BUƘATA TA MUSAMMAN (NAKASASSU)

Gwamnatin Jihar Kano, na ɗaya daga cikin jerin jihohin da su ka tabbatar da dokokin ba da dama da ƴancin naƙasassu su gudanar da dukkan ayyukansu ba tare da sun fuskanci duk wata tsangwama da kyara da nuna bambanci daga sauran al’umma ba.

Kuma idan kuɗurin dokar ya samu sahalewa nan gaba kaɗan za mu samar da ma’aikata ta musamman domin kula da su (nakasassu).

(7). FANNIN TSARO

Gwamnatinmu za ta tunkari dukkan wasu ƙalubale na tsaro da gaske, a yunƙurinmu na cigaba da kulawa da sa’ido, gwamnatinmu za ta gina wata cibiya ta musamman domin shawo kan matsalar tsaro cikin hanzari a hedikwatar tsaro ta Bomfai.

Sannan gwamnatinmu za ta samar da alaƙa mai ƙarfi tsakanin jami’an tsaro da kuma sauran al’umma fararen hula domin samun bayanan sirri da kuma kakkaɓe ƙalubalen tsaro daga makobta. Bugu da ƙari za mu samar da tsare-tsare na bayar da tallafi ga matasa domin kakkaɓe “zaman majalissa” da “jagaliya” da “daba”.

(8). ƘOƘARIN HUKUMAR YAƘI DA CIN-HANCI DA RASHAWA TA JIHA

Hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, ta na ɗaya daga cikin hukumomin yaƙi da rashawa na Jihohi da su ke aiki tuƙuru, ba kuma tare da katsalandan ɗin gwamnatin Jiha ba. Su na bin tsarin takwarorinsu na tarayya kamar (EFCC) da (ICPC). Kuma za mu sake ɗibar sabbin ma’aikatan hukumar kimanin mutum (145) waɗanda za a ba su horo a (EFCC) da (ICPC).

Kuma tuni wannan hukuma na kan binciken wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati waɗanda su ka yi handama da babakere da zarar an kammala bincike za a gabatar da su a gaban kotu.

(9). GINA YANKUNAN KARKARA

A ƙoƙarinmu na gina Jiha gaba ɗaya, za mu himmatu wajen gina yankunan karkara ta fuskar samar musu da tituna, da gidaje masu sauƙin farashi, gami kuma da samar da tsare-tsare masu kyau kan gonaki.

A wannan ƙoƙari da mu ke na cigaba da faɗaɗa cigaban wannan Jiha, manufarmu ta samar da ƙarin masarautu guda (4) zai taimaka matuƙa wajen wajen cigaba da maida yankunanmu birane a wannan Jiha.

(10). KAMMALAWA

Zan ƙara bayyana farin cikina da godiya ga al’umma kan sake zaɓata tare da matemakina a karo na biyu. Na yi farin ciki matuƙa.

Jihar Kano mu na da dukkan wani abin buƙata wajen haɓaka ta, ina kara kiranku gaba ɗaya ku zo mu haɗa kai wajen ƙarfafar manufofinmu na ciyar da wannan Jiha gaba.

Ina mai amfani da wannan dama wajen yabawa mai girma kakakin majalissar dokoki ta Jihar Kano, Hon. Kabiru Alhassan Rurum, tare da dukkan sauran ƴan majalissa gaba ɗaya. Da kuma sanatocinmu da ƴan majalissunmu na majalissar wakilai ta tarayya.

Ina kuma ƙara amfani da wannan dama wajen yabawa mataimakina, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, kan ƙoƙarinsa na cimma manufofin da mu ka sanya a gaba. Da alƙalin alƙalai na Jihar Kano, kan cigaba da inganta fannin shariya.

Ina kuma ƙara godewa al’ummar Jihar Kano kan yadda su ke cigaba da gamsuwa da ƙwarin gwiwarsu kan manufofin jam’iyyarmu”.

SHARHI

Haƙiƙanin gaskiya, samun gwamna kamar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na Jihar Kano, mawuyacin abu ne ta fuskar faɗa da cikawa, domin idan mu ka yi duba da dukkan alƙawura da fannonin da mai girma gwamna ya yi alƙawarin maida hankali akai cikin wannam zangon mulki, za mu fahimci kusan duk ya cimma su cikin kwanaki ɗari kacal.

Misali, fannin Ilimi da tsaro da na lafiya, har lambobin yabo na girmamawa ya samu daga ƙungiyoyi daban-daban daga ciki da wajen Nageriya dangane da ƙwazo da rawar ganin da ya taka.

Sannan alƙawari na farko da ya yi kan bayar da Ilimi kyauta tun daga Firamare har zuwa babbar sakandire shi ma gashi nan tuni mai girma gwamna ya ƙaddamar.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Nasarorin Ganduje

Za’a kaddamar da gidan rediyon gwamna Ganduje da zaku iya sauraro daga ko ina a duniya

Published

on

By

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Duk Nageriya, Gwamna Ganduje Ne Gwamna Ɗaya Tilo Da Aka Taɓa Samar Masa Gidan Rediyo A Yanar Gizo-Gizo.

-Gidan Rediyo Ne Da Zai Riƙa Gabatar Da Shirye-Shiryensa Kai Tsaye Har Tsawon Awanni Ashirin Da Huɗu Dare Da Rana A Kowacce Rana A Duk Mako.

-Sannan Kuma, Gidan Rediyon Zai Kasance A Ƙarƙashin Kulawar Ƙungiyar Ganduje New Media Promoters.

Yau Laraba, 20 ga watan Nobemba, 2019.
A wani mataki na cigaba da ƙara sanar da duniya ɗumbin ayyukan da mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya aiwatar a zangon farko na gwamnatinsa da kuma waɗanda ya ke cigaba da aiwatarwa a wannan zangon mulki na biyu, da kuma ƙoƙarinmu na ƙara himma wajen cigaba da ƙara ɗaga kima da darajarsa (gwamna Ganduje) a idon duniya, tuni mun kammala samar da katafariyar kafar watsa labarai ta Rediyo wacce za ta riƙa aiki na tsawon a wanni (24) a kowacce rana kai tsaye (Online).

Duk da kasancewar akwai ƴan gyare-gyare da mu ke cigaba da yi wa tashar a halin yanzu domin ƙara kyautata jin daɗin masu sauraro, cikin ikon Allah mu na farin cikin ƙaddamar da fara amfani da gidan Rediyon tayadda duk wanda ya buga adireshinmu na: www.gandujeonlinerediyo.com, zai zame mu kai tsaye.

Wannan ƙaddamarwa ce ta yadda mutane za su fara amfani da gidan Rediyon kai tsaye, daga bisani kuma akwai gagarumin taro na musamman da za mu shirya domin ƙaddamar da wannan gidan Rediyo a zahiri. Tayadda kuma hatta mutanen karkara da ke amfani da wayoyin hannu ƙanana ma za su iya kama gidan Rediyon su kuma saurari shirye-shiryenmu kai tsaye.

Haka zalika, gidan Rediyon zai kasance ne a ƙarƙashin kulawar ƙungiyar Ganduje New Media Promoters, a wani mataki na zaburar da matasa sanin amfani da fasahohin zamani da aikace-aikacen kimiyya da fasaha.

Mun tanadar muku shirye-shirye na musamman masu armashi da gamsarwa kan ɗumbin nasarori da managartan ayyukan mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sannan akwai ɗumbin waƙoƙi na mawaƙan mai girma gwamna daban-daban waɗanda su ma za mu riƙa sanya muku domin ƙayatar da ku da kuma ɗebe muku kewa a kowane lokaci.

Ganduje Online Rediyo ita ce kafar watsa labarai ta farko mai watsa shirye-shiryenta kai tsaye wacce aka taɓa samarwa wani gwamna a tarihin gwamnonin Nageriya gaba ɗaya na da da na yanzu. Za ku iya sauƙe manhajarmu a Play Store, ko ku latsa wannan kai tsaye domin sauƙewa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.gandujeonlineradio.com

Mu na fatan jama’a za su rungumi wannan gidan Rediyo hannu bibbiyu domin samun ƙayatattun shirye-shirye masu armashi da gamsarwa gami kuma da ƙayatarwa a kowane lokaci. Mun gode.

Continue Reading

Nasarorin Ganduje

An zabi gwamna Ganduje uban kungiyar Fulani ta Africa

Published

on

By

ƘUNGIYAR FULANI MAKIYAYA TA NAHIYAR AFRIKA TA ZAƁI GWAMNA GANDUJE A MATSAYIN BABBAN UBA A ƘUNGIYAR

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Yau Juma’a 25 ga watan Octoba, 2019.
Haɗakar fulani makiyaya daga Nahiyar Turai da ƙasar Amurka waɗanda tushiyarsu ta ke a Nahiyar Afrika, sun zaɓi mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin babban uba ga ƙungiyar, tayadda kuma ya zamto ɗan Afrika na farko da ya ya taɓa samun wannan matsayi a ƙungiyar.

Ƙarƙashin ƙungiyar ta fulani maƙiyaya ta Nahiyar Afrika kan zaman lafiya da samar da cigaba, ofishinsu mai lamba 12121, kan titin Audia kusa da gini mai lamba 2308, Dallas Tx 75243, a ƙasar Amurka. Sai kuma ofishinsu mai lamba, 4 Sambo Close, Badiko Jihar Kaduna a Nageriya.

Ƙungiyar ta kuma yabawa mai girma gwamna kan yadda ya ke maida hankali wajen kyautata rayuwar Fulani makiyaya a ƙasashen Nahiyar Afrika gaba ɗaya.

A wasiƙar da su ka aikewa mai girma gwamna mai ɗauke da sa hannun babban sakataren ƙungiyar, Muhammad Farouƙ Auwalu, kan shaida masa wannan zaɓa tasa da su ka yi, sun yi bayani cewa:

“mai girma gwamna, ƙoƙarin da ka ke a gwamnatinka, domin kyautata rayuwar fulani makiyaya a Nageriya, ba shakka ka cancanci yabo daga wannan ƙungiya tamu, saboda waɗannan dalilai, mu ka ga dacewar mu nemi ka zama babban uba ga wannan ƙungiya”.

Dangane da ƙoƙarin mai girma gwamna wajen samar da Rugar zamani ga fulani makiyaya, ƙungiyar ta buƙaci samun damar ganawa da shi mai girma gwamna domin tattauna “muhimman batutuwa, masu alaƙa da fulani makiyaya da kuma sabon tsarin da za a tunƙara wanda zai wanzu ya kuma gamsar da su (Fulanin)”.

Sannan su ka yi ƙarin bayani da cewa a mtsayinsu na ƙungiya za su yi duk mai yiyuwa wajen samar da mafita kan zirga-zirgar fulani makiyaya a Nahiyar Afrika. Kuma za su ba da shawarwari kan yadda za a riƙa alkintawa Fulani makiyaya wurin kiwo a Nageriya da ma Afrika gaba ɗaya.

Daga nan kuma sai su ka labartawa mai girma gwamna yadda haɗakar aiki tare za ta taimaka da kuma yadda su ke da ƙarfin gwiwa cikin fatan ya amince da wannan buƙata tasu a gare shi.

“Ƙungiyarmu ta Fulani makiyaya ta Nahiyar Afrika kan zaman lafiya da samar da cigaba, mu na zaɓar mutum ne mai nagarta da daraja wanda ya ke shimfiɗa shugabnci nagari ga fulani makiyaya a Nahiyar Afrika kowane lokaci. Wanda kuma ya ke ƙoƙari da fafutuka a kansu”.

“Mai girma gwamna, kasancewarka babban uba ga wannan ƙungiya, zai taimaka mana matuƙa wajen samun nasarar cimma manufofi da muradan wannan ƙungiya kan fafutukar kare haƙƙin fulani makiyaya a Nahiyar Afrika.

Inda kuma su ka ƙara da cewa: “wannan zai samu ne ta hanyar ƙara samar da haɗin kai da sauran gwamnonin Arewa da sassan hukumomin samar da cigaba na Duniya da kuma dukkan masu ruwa da tsaki kan wannan gwagwarmaya. Mu na cike da fatan mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai samar da kykkyawan jagorancin da ake buƙata wajen cimma manufofi da muradan da wannan ƙungiya ta sanya a gaba.

Continue Reading

Nasarorin Ganduje

Kano9: Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin bincike kan satar yaran Kano

Published

on

By

GWAMNA GANDUJE YA ƘAFA KWAMITI MAI ƘARFI DOMIN GUDANAR DA BINCIKEN ƘWAƘWAF KAN BADAƘALAR SATAR YARA A JIHAR KANO

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Gwamna Ganduje Ya Kuma Umarci Kwamitin Da Ya Kawo Cikakken Rahoton Mutanen Da Aka Rasa Tun Daga Shekarar (2010) Zuwa Yau (2019) A Jihar Kano.

Yau Juma’a, 25 ga watan Octoba, 2019.
A wani mataki na ƙoƙarin bin haƙƙoƙin yara (9) da aka ceto bayan an yi garkuwa da su an kai su Jihar Anambara, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi domin gudanar da binciken ƙwaƙwaf a ƙarƙashin jagorancin tsohon mai shari’a Wada Umar Rano, kuma mai girma gwamna zai ƙaddamar da kwamitin a ƙarshen wannan wata ranar Alhamis, 31 ga watan Octoba, 2019.

Daga cikin ayyukan da kwamitin zai gudanar, sun haɗa da: bincike mai zurfi kan adadin mutanen da aka rasa daga shekarar (2010) zuwa yau a Jihar Kano tare da gabatar da dukkan hujjoji sahihai rubutattu ko na fatar baka da dukkan wani mutum da za a iya ganewa a matsayin hujja inda yiyuwar hakan.

Daga cikin hujjojin da kwamotin zai yi la’akari da su har da gayyato duk wani mutum a Nageriya da ke da wata hujja ya halarci duk wani taro da membobin kwamitin ya gabatar da hujja ko ya miƙa duk wasu rubutattun bayanai ko duk wata alama ko abubuwa na hujja (a rubuce ko da baki) a mtsayin duk wata hujja da zai iya rantsewa akai ingantacciya ce.

Sauran hanyoyin da za su yi la’kari da su wajen tattara hujjojin har ganawa ko tattaunawa da wani mutum ko wasu mutane ko ƴan jarida domin samar da kammalallu kuma ingantattun bayanai kan mutanen da aka rasa a Jihar Kano daga wancan lokaci da aka bayyana zuwa yau.

Bayan sun kammala tattara bayanan kan yawan mutanen da aka rasa da kuma dalilan da ke haifar da hakan, kai tsaye kwamitin zai miƙa rubutaccen rahoton sakamakon bincikensa ga gwamnatin Jihar Kano.

Idan dai za a iya tunawa a kwana-kwanannan rundunar ƴan sanda ta ƙasa shiyar Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin amintaccen shugaban rundunar (CP) Ahmed Iliyasu ba ta kai ga kammala warware matsalolin yaran da aka sace a Jihar Kano ba.

Jimillar yaran su tara ƴan shekaru 2 zuwa 10 da aka yi garkuwa da su, 8 daga cikinsu an sayar da su ne a Farawa da ke Jihar Anambara. Wasu daga cikin waɗanda iftila’in ya afkawa sun kasance ne a matsayin bayi fiye da tsawon shekaru biyar a Jihar ta Anambara inda aka sauya musu yanayinsu na ainahi.

Sashe na biyu na doka kan kwamitin binciken cikin baka ta (CAP.29) a dokokin Jihar Kano na (1990) ya ba wa mai girma gwamna cikakkiyar dama da ikon kafa wannan kwamiti na bincike.

Dangane da wannan batu, gwamna Ganduje ya byyana cewa: “a hukumance mu na sanar da al’umma membobin wannan kwamiti gaba ɗaya nauyin da mu ka ɗora musu na gudanar da bincike mai zurfi kan matsalar ɓatan al’umma a Jihar Kano daga shekarar (2010) zuwa (2019) da su ka shafi 30 ga watan Octoba, 2019 da kuma 30 ga watan Nuwamban 2019”.

Da ya ke bayyana farin cikinsa kan yara taran da aka gano aka kuma miƙa su ga iyayensu, ya bayyana cewa gwamnatinsa “za ta cigaba da tunkarar wannan barazana ta tsaro da muhimmanci domin daƙile ta gaba ɗaya”.

Kuma Kwamitin zai saurari ɓangaren waɗanda matsalar ta shafa domin tattara hujjoji na baki da kuma rubutattu. Sannan kuma za su duba yiyuwar ziyartar wurin da lamarin ya faru, sannan gwamnati za ta tabbatar da ta yi duk mai iyuwa wajen magance dukkan ire-iren waɗannan matsaloli.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending