Connect with us

Kano A Mako Mai Karewa

JIHAR KANO A MAKO MAI ƘAREWA (18) -Bashir Abdullahi El-bash

Published

on

JIHAR KANO A MAKO MAI ƘAREWA (18)

TSARAWA DA GABATARWA Bashir Abdullahi El-bash

-A Wannan Mako Mai Ƙarewa, Gwamna Ganduje Ya Na Gudanar Da Ziyarar Aiki A Ƙasar Amurka Kan Sha’anin Kiwon Lafiyar Al’umma.

-A Wannan Mako Mai Ƙarewa, Fulani Makiyaya Sun Fara Amfana Da Rugar Zamani Da Gwamna Ganduje Ya Ke Ginawa A Wannan Jiha, Inda Tuni Aka Samar Da Famfunan Ruwa Masu Amfani Da Hasken Rana Guda Biyar.

A ƙarshen makon da ya gabata, mun ji yadda mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin Kwamishinoninsa a zangon mulki na biyu, sannan kuma ya gabatar da kasafin kuɗin shekara mai zuwa (2020) a gaban zauren majalissar dokoki ta Jiha.

Haka zalika, mun ji yadda kamfanin mai na ƙasa (NNPC) ya karrama ƴar mai girma gwamna, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje (Ƴar Aljannah) da lambar yabo ta girma sanadiyyar lashe gasa da ta yi a matakin ƙasa gaba ɗaya.

Haka nan mun ji yadda mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƴan kasuwa da masu masana’antu ta Jiha kan wa’adin zangon mulki na biyu.

Yau Juma’a, 15 ga watan Nobemba, 2019.
Kamar yadda aka saba, a wannan mako ma ga ni tafe da wani sabon shirin wanda a bisa al’ada Ni Bashir Abdullahi El-bash na saba kawo muku muhimman batutuwa masu alaƙa da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatinsa waɗanda su ka faru a makon da mu ke daf! Da yin bankwana da shi.

(1). A wannan mako mai ƙarewa, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shugabanci nagari a matsayin babban ginshiƙi abin lura wajen cimma dukkan wasu nasarori da muradun da aka ƙirƙiro.

Gwamna Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana hakan ne a ya yin da ya ke gabatar da jawabi a Otel ɗin Sheraton, da ke birnin tarayya Abuja, a ya yin taron ƙaddamar da littafi mai taken: (The Challenges Of Good Governance In Nigeriya), Ƙalubalen shugabanci nagari a Nageriya”, wanda tsohon gwamnan Jihar Osun, Chief Bisi Akande ya rubuta

Shi ma a nasa jawabin, Chief Bisi Akande, ya bayyana gwamna Ganduje a matsayin tsayayye kuma jajirtaccen ɗan siyasa wanda ya taka gagarumar rawa wajen samun nasarar jam’iyyar (APC) a babban zaɓen shekarar 2015.

(2). A saƙon da ya aike albarkacin ranar Maulidi, a wannan mako mai ƙarewa, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya hori al’ummar musulmai gaba ɗaya da su zamto masu koyi da kuma ɗabbaƙa kyawawan halaye da ɗabi’un da manzon Allah (S.A.W) ya koyar a kowane lokaci a ɗaiɗaikunsu da kuma jimmalace a cikin al’umma gaba ɗaya.

Gwamna Ganduje ya ƙara da bayyana cewa ranar Maulidi rana ce da ake gudanar da shagulgulan bikin murnar zagayowar ranar da aka haifi manzon tsira, fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W) dan haka ka da ranar ta zamto ranar tuni kawai, ta zamto ranar tuni da kuma ɗabbaƙa kyawawan halaye da ɗabi’un da manzon Allah, (S.A.W) ya koyar a aikace a dukkan harkokinmu na yau da kullum.

“Aiwatar da nagartattun halaye da ɗabi’un manzon Allah (S.A.W) na gaskiya, haƙuri, juriya, adalci, aiki tuƙuru, tarbiyya, kyauta, karamci, mutuntawa, martabawa, a dukkan lamuranmu, shi ne mafita kan matsalolinmu a ɗaiɗaikunmu da kuma a jimlace”. Inji Gwamna Ganduje.

Daga nan kuma sai gwamna Ganduje ya ƙara yin kira ga al’ummar musulmai da su yi amfani da wannan dama wajen cigaba da yi wa Jihar Kano da ƙasa gaba ɗaya addu’ar cigaba da samun zaman lafiya da ƙaruwar arzuƙi mai ɗorewa.

(3). A wannan mako mai ƙarewa, a cigaba da ƙoƙarin da ya ke na magance matsalar zirga-zirgar fulani makiyaya zuwa sassan wannan ƙasa da ma haurawarsu sassan ƙasashe maƙoɓta wacce ke haifar da cikas kan sha’anin tsaro, da kuma fatan da ya ke na kawo sauyi kan tsarin kiwo daga batu irin na al’ada zuwa ga batu na tattalin arziƙi, tuni yanzu haka mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya samar da famfunan ruwa kimanin guda 5 masu amfani da hasken rana a dajin Dansoshiya inda a nan ne zai gina rugar zamani ga fulani makiyaya a wannan Jiha.

Kuma tuni yanzu haka fulani makiyaya har ma sun fara amfani da waɗannan famfuna wajen shayar da dabbobinsu ruwa a wannan daji na rugar zamani.

Sannan akwai aikin samar da gidaje kimani guda (200) da kuma gidaje na musamman guda (3) masu ɗakuna bibbiyu da ɗakin dafa abinci da kuma na ajiye kaya da makewayi (banɗaki) su ma su na nan ana cigaba da samarwa.

“Daɗi da ƙari, akwai kuma tankin tara ruwa (dam), mai girman sama da (100,000m3) wanda shi ma yanzu haka ana kan aikin samar da shi, wanda kuma masana su ka samar da yanayinsa, tayadda za a yi amfani da shi da kuma ƙididdige sauran abubuwan da ake buƙata”. Cewar Dakta Jibirilla Muhammad, shugaban kwamitin da gwamna Ganduje ya kafa dangane da duba da kuma nazarin wurin samar da rugar.

Tuni an yi nisa kan aikin gyaran muhallin da za a yi dam ɗin, inda yanzu haka ya kai kusan kaso tamanin (80%), haɗe kuma da samar da titi da asibitin kula da lafiyar dabbobi da ta kula da lafiyar mutane da kuma aikin samar da makarantar firamare da ofishin ƴan sanda da kasuwa da sauransu waɗanda dukkaninsu ana daf da fara aikwatar da aikinsu.

Ɗaya daga cikin fulani makiyaya da ake kira da suna Suleman daga Kwanar Ɗangora, ya yabawa gwamna Ganduje kan wannan kykkyawan tunani nasa, sannan kuma sai ya ƙara da yin kira ga fulani makiyaya da su dawo Jihar Kano domin gudanar da kiwo rani da damina.

Sannan ya kuma ƙara da cewa “aikin zai taimaka matuƙa wajen ƙara ƙarfafa yanayin halin tsaro da zaman lafiyar da jihar Kano ta ke ciki wadda kuma za ta taimaka wajen haifar da mafita ta ƙarshe kan rikice-rikicen fulani makiyaya da manoma.

Wani bafulatani makiyayin mai suna Moddibbo Bello, ya yaba da cewa “Kafin wannan lokaci, mu na yin tafiya mai nisa wajen shayar da dabbobinmu ruwa, sannan da rani mu kan yi ƙaura zuwa kudancin Nageriya da ma haurawa har zuwa sassan ƙasashe maƙoɓta, sai dai a yanzu babu wani wuri da za mu tafi”.

(4). A cigaba da ƙoƙarin gwamnatin mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan kyautata harkokin noma a wannan Jiha, a wannan mako mai ƙarewa, mai girma mataimakin gwamna, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna tare da kwamishinan gona na jiha sun ziyarci cibiyar bincike kan harkokin noma da ke birnin tarayya Abuja domin samar da dangantakar aiki tare wajen bunƙasa bincike kan harkokin noma a wannan Jiha.

(5). A wannan mako mai ƙarewa, mai girma gwmnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya na ziyarar aiki a ƙasar Amurka tare da takwarorinsa gwamnoni inda su ke gudanar da taruka kan harkokon lafiya da kuma samo ƙarin cigaba da alkhairai ga wannan Jiha.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending