Connect with us

Labarai

JAMI’AN TSARO SUN SAMU NASARAR KAME WANDA YA SHIRYA AURAR DA FATIMA GANDUJE TA BOGI

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Ya Samar Da Fatima Ganduje Ta Bogi Ya Karɓi Kuɗi Kimanin Naira Miliyan Biyar Da Sunan Zai Ba Da Auren Fatima Ganduje Ta Gaske.

-Iyalan Gwamna Ganduje Sun Ba Da Umarni Jami’an Tsaro Su Cafke Duk Wani Ko Wata Da Za Su Bayyana Kansu A Matsayin Yaran Gidan Su Damfari Al’umma.

Yau Asabar, 23 ga watan Nobemba, 2019.
Jami’an tsaro sun samu nasarar kame wani matashi mai suna Abdullahi Zakari, wanda ya bayyana kansa a matsayin yaron gidan mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya damfari wani mutum mai sana’ar saida magunguna mai suna Alhaji Bashir Amadu Usaini da ke unguwar Tudun Yola zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan Biyar da sunan wai zai haɗa shi da ƴar mai girma gwamna Fatima Ganduje ya aura.

Yadda lamarin ya faru shi ne: tun kafin Fatima Ganduje ta yi aure, Abdullahi Zakari ya samu wani mai suna Alhaji Bashir Amadu ya kwaɗaita masa cewar shi yaron gidan gwamna Ganduje ne, dan haka ya yi masa alƙawarin zai haɗa shi aure da Fatima Ganduje. Sannu a hankali har ta kai ga wannan ɗan damfara (Abdullahi Zakari) ya samar da Fatima Ganduje ta ƙarya ya haɗa su da Alhaji Bashir Amadu su na waya da juna da sunan soyayya.

Sannu-sannu har ta kai ga wannan Fatima ta bogi ta na neman kuɗi a wurin Alhaji Bashir Amadu inda ta ke shaida masa cewar wai auren dole za a yi mata a gida, dan haka ba ta tambayar kowa kuɗi in ba shi ba, saboda shi ta ke so ta aura.

Sannan kuma, shi wannan ɗan damfara ya samar da wata matar ta bogi a matsayin Balaraba Ganduje, wato yayar Fatima Ganduje, ta yadda duk kuɗin da Fatima Ganduje ta bogi za ta nema a wurin Alhaji Bashir Amadu, ita wannan Balaraba Ganduje ta bogin ce ta ke ƙara ba shi tabbacin da ƙarfin gwiwa kan ya ba da ko nawa ne ta tambaye shi saboda wai ita Fatiman ba ta tambayar kowa kuɗi a gidan nasu sai shi saboda shi ne ta ke son zai aure ta, wanda hakan ne kuma ya ke sanya shi ko da yaƙi ko kuma ba shi da kuɗi a lokacin to wannan ƙaimi da Balaraba Ganduje ta bogin ta ke yi masa kan sa shi ya nemo ya bayar.

Bayan haka, shi dai wannan ɗan damfara, har Gwaggo wato Hajiya Gafsat Ganduje ya samar ta bogi, inda ya sanya ita waccar Fatiman bogin ta nemi wayar mahaifiyar shi wanda ake damfara ɗin, Bashir Amadu ta haɗa su da wannan Gwaggo ta bogi su ka gaisa da mahaifiyarsa a lokacin da ba ta da lafiya.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da Fatima Ganduje da Balaraba Ganduje da kuma (Gwaggo) Hafsat Ganduje duk na bogi kafin Fatima Ganduje ta gaske ta yi aure har tsawon kusan shekaru uku.

Sannan bayan Fatima Ganduje ta gasken ta yi aure, duk da haka ba su ƙyale shi ba, wannan Fatima Ganduje ta bogin ta cigaba da yi masa waya ta na faɗa masa cewar ita fa ba zaman auren nan za ta yi ba domin dole aka yi mata dan haka za ta kashe auren ta fito ta aure shi.

Haka wannan matashi mai suna Abdullahi Zakari, ya yi ta amfani da waɗannan mata a matsayin ƴaƴa ne na gwamna, wato Fatima da Balaraba, da kuma mahaifiyarsu Gwaggo ya yi ta karɓan kuɗi a hannun wannan bawan Allah mai suna Bashir Amadu Usaini har kimanin Naira Miliyan Biyar cikin shekaru uku da su ka shafe.

Sai dai jami’in tsaro sun samu nasarar kame wannan ɗan damfara, har ma an gurfanar da shi a gaban kotun Noman Salak da ke nan Jihar Kano a jiya, kuma alƙali ya tura shi zaman gidan kaso kafin a nemo sauran matan da ya yi amfani da su wajen shirya wannan damfara da zamba a dawo a cigaba da shari’ar.

Sannan kuma tuni iyalan mai girma gwamna sun ba da gargaɗi kan a guji yarda da duk wani wanda zai je wa da wani da irin wannan alaƙa, sannan kuma duk wanda aka kama to ayi gaggawar sanar da jami’an tsaro mafi kusa domin su kame shi.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Majalissar Zartarwa Ta Amince  A Kafa Ƙarin Masarautu Guda Huɗu U A Jihar Kano 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Kuma Tuni Ta Tura Ƙudirin Dokar Zuwa Gaban Zauren Majalissar Dokoki Na Jihar Kano.

Yau Litinin, 2 ga watan Disamba, 2019.
A wani zama da ta gudanar a daren Jiya Lahadi, majalissar zartarwa ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da ƙudirin dokar kafa ƙarin masarautu guda huɗu a Jihar Kano. Waɗanda su ka haɗa da masarautar: Bichi da Gaya da Rano da kuma Ƙaraye. Inda tuni kuma majalissar ta tura ƙudirin dokar zuwa gaban zauren majalissar dokoki na Jiha.

Sanarwar da aka fitar daga gidan gwamnati, ta kuma ƙara yin bayani da cewa dama can akwai wasu daga cikin waɗannan masarautu tun shekarun baya masu tsawo da su ka wuce, juyin zamani ne ya nemi ya shafe tarihinsu, kuma ko a zamanin janhoriya ta biyu sai da aka nemi a farfaɗo da su, amma aka samu tsaiko.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa majalissar zartarwa ta tattauna sosai game da alfanun ƙarin nasarautun kafin ta cimma wannan matsaya da ta ɗauka, ta kuma fahimci cewa ƙarin masarautun zai taimaka sosai wajen ƙara kusanci a tsakanin al’umma da sarakunan gargajiya. Sannan kuma ƙarin masarautun zai taimaka matuƙa wajen ƙara haɓaka harkokin kasuwanci da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Kano cikin hanzari.

Haka zalika, ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na ilimi kyauta kuma wajibi tun daga firamare har zuwa babbar sakandire, ya na buƙatar taka rawar al’umma sosai da sosai musamman ma sarakunan gargajiya domin samun nasarar shirin. Dan haka ƙarin masarautun zai taimaka sosai da sosai wajen cimma wannan buri.

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa ƙudirin dokar da aka ɗabbaka a zauren majalissaar dokoki a 2019, kotu ta rushe shi ne saboda mutum ne daga cikin al’umma ya gabatar da shi ba ɗaya daga cikin ƴan majalissa ba.

Kamar yadda sanarwar ta ƙara, majalissar zartarwar ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta kuma buƙaci zauren majalissar dokokin na Jihar Kano da su yi duba da buƙatun al’umma wajen amincewa da ƙudirin dokar.

Continue Reading

Labarai

Gwamna Ganduje Ya Taya Mallam Ibrahim Shekarau Murnar Samun Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa 

Published

on

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-“Lambar Yabo Ta Digirin Girmamawa Da Aka Ba Wa Sanata Shekarau Alama Ce Da Ke Ƙara Shaida Yadda Duniyar Ilimi Ta Gamsu Da Irin Ɗumbin Gudunmawar Da Ya Ba Ta A Zamanin Da Ya Riƙe Matsayin Gwamna Da Muƙamin Ministan Ilimi Na Nageriya”. Inji Gwamna Ganduje.

Yau Asabar, 30 ga watan Nobemba, 2019.
Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano hawa biyu, kana kuma sanata mai ci, Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano murnar samun lambar yabo ta digirin girmamawa wanda Jami’ar Ritman da ke birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom ta ba shi a wannan rana ta Asabar.

Digirin girmamawar wacce jami’ar ta ba shi saboda irin ɗumbin gudunmawar da ya bayar a fannin iilimi a zamanin ya na matsayin gwamna da matsayin ministan ilimi, gwamna Ganduje ya taya shi murna a madadin gwamnatin Jihar Kano da al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya.

Kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar taya murnar da gwamna Ganduje ya bayar, “mai girma gwamna ya ga lambar yabo ta digirin girmamawa da aka ba wa Sanata Ibrahim Shekaru, inda lambar ke ƙara shaida yadda fannin ilimi ya gamsu da irin ɗumbin nasarori da gudunmawar da ya bayar a fannin da kuma gina rayuwar ɗan adam a lokacin da ya riƙe matsayin gwamna da kuma Ministan Ilimi a Nageriya.

Idan za a iya tunawa, ko a shekarar 2009, Sanata Shekarau ya samu irin wannan lambar yabo ta digirin girmamawa daga Jami’ar ƙasa ta Nsuka”. Sanarwar ta bayyana.

Inda kuma gwamna Ganduje ya ƙara da cewa wannan lambar yabo ga sanata Shekarau tambar ƙara zaburar da shi ne ya ƙara himma da ƙoƙari kan ƙoƙarin da ya ke na ba da gudunmawa wajen gina ƙasa da kuma gina rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Ya yin da ya ke taya Sanata Shekarau murnar wannan ƙarin matsayi da ya samu, gwamna Ganduje ya yi masa fatan alkhairi tare da fatan ya ƙara cigaba da dagewa wajen ba da gudunmawa kan cigaban ƙasa da sauran jama’a.

Continue Reading

Labarai

Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II sun gana da ‘yan kasuwa a China

Published

on

By

GWAMNA GANDUJE TARE DA SARKIN KANO SUN GANA DA ƳAN KASUWA MASU ZUBA JARI NA ƘASAR CHANA

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Sun Haɗu Sun Tattauna A Jihar Legas, Kuma Nan Gaba Kaɗan Za Su Je Ƙasar Ta Chana

Yau Laraba, 6 ga watan Nobemba, 2019.
A wani mataki na haɗuwar kai domin samo ƙarin cigaba, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tare da mai martaba sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sunusi Lamiɗo Sunusi na biyu, sun gana da shugaban kwamitin Shandong Provincial wanda ya jagoranci babbar tawagar wakilan ƴan kasuwa masu zuba jari na ƙasar Chana inda su ka tattauna kan fannin amfanin da kowa zai samu cikin hulɗar kasuwancin da su ka ƙulla.

Gwamna Ganduje ya shaidawa wakilan da su ka zo daga ƙasar ta Chana cewa : “akwai fa’ida ga kowannenmu. Kuma Shandong Province zai maida hankali ne kan waɗannan fannoni domin gina masana’antunmu. Waɗannan fannoni su ne na : Fatun dabbobi da kayan saƙa da kayan noma, musamman shinkafa da alkama da injinan aikin gona da kuma ma’adanan ƙarƙashin ƙasa.

Taron tattaunawar ya gudana ne a Raddison Blue Hotel Victoria Island da ke birnin Legas a wani mataki na shirye-shiryen zuwa ƙasar ta Chana tare da mai martaba sarkin Kano wanda ya ke matsayin shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin kasuwanci da shigo da masu zuba jari na Jihar Kano, ya yin kuma da mataimakin gwamna zai jagoranci tawagar wakilai daga Kano.

Kamar yadda gwamna Ganduje ya faɗa, “Jihar Kano jiha ce da ke matuƙar jan hankalin masu zuba jari. Tare da yawan al’ummarmu, mun kasance jiha mafi yawan al’umma a wannan ƙasa, sannan Jihar Kano cibiya ce ta kasuwanci ba ga Nageriya kawai ba, harda sauran ƙasashe maƙobta na Nahiyar Afrika, abu ne a bayyana duk wanda ya zuba jari a jihar Kano ya na da kasuwa mai ɗorewa” Inji gwamna Ganduje.

Dangane da zaɓar mai martaba sarkin Kano kan matsayin shugaban kwamitin ba da shawara kan kasuwanci da zuba jari, gwamna Ganduje ya bayyana cewa “sarki mutum ne mai himma da ƙwarewa kan harkokin tattalin arziƙi da mutunta ƴan kasuwa na ƙasashen duniya, zai taika muhimmiyar rawa wajen cimma wannan buri”. Gwamna Ganduje ya bayyana.

Gwamna Ganduje ya kuma buƙaci shugaban na Shandong da su yi la’akari da fannin ilimin jiha domin ya na daga cikin fannonin yarjejeniyar da aka ƙulla a tsakaninsa da jihar Kano, kamar yadda ya ke cewa : “batun kyautata cigaban ilimi na daga cikin sassan fannonin da za mu yi aiki a kai tare da batun ba da horon sana’o’i da na ilimin fasahohin sadarwar zamani da kuma shirye-shirye kan musayar ilimi”. Cewar gwamna Ganduie.

“Ina godiya a gare ku a madadin al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya kan yadda ku ka sanya hannu kan yarjejeniyar da mu ka ƙulla wacce mataimakina ya wakilce ni wurin taron sanya hannun”. Inji gwamna Ganduje.

Shi ma a nasa jawabin, mai martaba sarkin kano ya bayyana godiyarsa ga tawagar wakilan na Chana, inda kuma ya ƙara da tunatar da su cewa : “Duniya a yau ta na magana ne kan batun kyautata wutar lantarki da kuma wuta mai amfani da hasken rana duk waɗannan na daga cikin manyan muhimman fannoninmu”.

“A tare da goyon bayan kano da shandong za mu samu nasarar samun ƙasar da aka alƙawarta idan mu ka fara ziyartar ƙasar Chana ƙarƙashin wannan shiri za mu tabbatar tare da mai girma gwamna mun yi iya ƙoƙarinmu wajen tabbatar da nasarar wannan yunƙuri”.

Bayan sarki sauran tawagar gwamna ganduje sun haɗa da shugaban ma’aikata na gidan gwamnati mallam Ali Makoɗa da sarkin shanun Kano Alhaji Shehu Usma Muhammad da manajan daraktan masana’antu da muhalli Dakta Jibirilla Muhammad da kuma na hukumar cigaban masanaantu ta jiha Lawan Alhassan da kuma daraktan kasuwanci na maaikatar harkokin kasuwanci Abdullahi Idris.

Daga ɓangaren wakilan na chana bayan shugaban na shandong akwai Liu Yongju babban sakataren shandong sai mista Li Yongsen mataimakin darakta da mista Zhang Xigcheng jami’in bincike sai Zhao Qing sai kuma wakilai daga SDDAO da SDDOC.

Sannan akwai tattaunawar za ta cigaba gobe a nan Kano inda za su gana da ƙungiyoyi kan harkokin cigaba da ƙulla dangantakar kasuwanci.

Continue Reading

Listening Live

Note: Fasaha Radio tana aiki tsawon awanni 24 domin wayar da kan al'umma akan yadda ake amfani da fasahar zamani.

Bangarori

Trending